Adam Fakai: Fitaccen Masoyin Tinubu a Arewa Ya Dakatar da Tallata Ayyukan Gwamnati
- Wani fitaccen masoyin Bola Tinubu a Kebbi, Adam Fakai, ya dakatar da tallata ayyukan gwamnatin tarayya bayan fiye da shekara biyu yana yi da kuɗinsa
- Adam Fakai ya ce bai samu wata kulawa ko goyon baya daga shugabannin APC a Kebbi ko matakin tarayya ba duk da ƙoƙarinsa wajen yaɗa ayyukan Tinubu
- Amma ya ce hakan ba ya na nufin ya daina goyon bayan Tinubu ba, illa dai dakatar da aikin tallata gwamnati saboda halin ko in kula da aka nuna masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Kebbi – Wani fitaccen masoyin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a jihar Kebbi, Adamu Yahaya, wanda aka fi sani da Adam Fakai, ya sanar da janyewarsa daga aikin tallata manufofi da ayyukan gwamnatin tarayya.
Adam Fakai ya ce ya yanke wannan shawarar ne saboda rashin kulawa da goyon baya daga jam'iyyarsa, da halin ko in kula daga masu ruwa da tsaki a gwamnati.

Source: Twitter
"Da kudina nake tallata Tinubu - Adam Fakai
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na TikTok, Adam Fakai ya ce ya shafe fiye da shekaru biyu yana amfani da kudinsa, lokacinsa da karfinsa wajen yada ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ga al'ummar Najeriya, musamman a Arewacin Najeriya.
Ya bayyana cewa ya gudanar da wannan aiki ne saboda imaninsa cewa gwamnatin Tinubu na kokarin gina Najeriya ta fuskar ci gaba da ayyukan raya kasa.
“Na shafe fiye da shekaru biyu ina amfani da kudina, lokacina da karfina wajen yada ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga al'ummar Arewa da Kudu. Na yi hakan ne saboda na yi imani da kokarin da yake yi wajen gina Najeriya,” in ji Adam Fakai.
Sai dai ya ce duk da irin gudunmawar da ya bayar, bai samu wata kulawa ko karfafa gwiwa daga shugabannin jam'iyyar APC a jihar Kebbi ko daga matakin tarayya ba.
Adam Fakai ya daina tallata gwamnatin Tinubu
A cewarsa, babu wanda ya nuna masa godiya ko ya ba shi wani tallafi domin ci gaba da aikin wayar da kan jama'a game da manufofi da ayyukan gwamnatin.
Ya kara da cewa:
“Ni dan jihar Kebbi ne, kuma a tsawon wannan lokaci ban taba samun wata kulawa, karfafawa ko goyon baya daga 'yan siyasar jam'iyyata a jiha ko a tarayya ba.
“Abin takaici ne yadda za ka ga wasu daga cikin manyan mutane daga tarayya suna amfani da hotuna ko bidiyon ayyukan shugaban kasa da na dauka suna yadawa, amma babu wanda ya taba tuntubata kai tsaye."
Adam Fakai ya kuma yi zargin cewa da a ce daga wata jiha daban ya fito, watakila da ya samu karin goyon baya saboda irin aikin da yake yi.
Ya bayyana cewa saboda abin da ya kira halin ko in kula da aka nuna masa, ya yanke shawarar dakatar da aikin tallata gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Duk da haka, ya gode wa duk wadanda suka taba karfafa masa gwiwa ta hanyar addu'o'i ko kalaman yabo a lokacin da yake gudanar da aikin.
Yadda Fakai ke tallata manufofin Tinubu
Wani bincike ya nuna cewa Adam Fakai ya shahara wajen ziyartar manyan ayyukan gwamnatin tarayya a sassa daban-daban na kasar nan tare da yada bayanansu a kafafen sada zumunta.

Source: Facebook
Daga cikin ayyukan da ya rika wallafawa akwai manyan tituna, ayyukan more rayuwa da shirye-shiryen gwamnatin tarayya da nufin wayar da kan jama'a kan manufofin gwamnatin APC.
An yi kokarin samun martani daga shugabannin jam'iyyar APC a jihar Kebbi da kuma jami'an gwamnatin tarayya dangane da kalaman Adam Fakai, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu wata amsa ba.
Duba sanarwar Adam Fakai a nan kasa:
An rotsa mai tallata Tinubu a Delta
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Delta ta umarci jami'an tsaro su gano tare da kama mutanen da suka kai hari kan Simon Mudi, hadimin gwamna Sheriff Oborevwori.
An kai wa hadimin gwamnan harin ne yayin taron masu ruwa da tsaki na APC a Delta ta Tsakiya, inda aka ji wa Simon Mudi da wasu raunuka masu tsanani.
Tsohon minista Solomon Dalung ya ce Simon Mudi na ci gaba da samun sauki, yana kuma godiya ga 'yan Najeriya da suka yi masa addu'a da nuna goyon baya.
Asali: Legit.ng


