Bayan Wata 6 a Hannun Yan Bindiga, Mutane 176 da Aka Sace a Kwara Sun Kubuta
- Gwamnatin Kwara ta sanar da cewa mutane 176 da aka sace yayin harin Woro da Nuku a Fabrairun 2026 sun samu 'yanci
- Gwamnatin ta yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, jami'an tsaro da duk waɗanda suka taka rawa wajen nasarar ceto mutanen, tana bayyana godiya ga kokarinsu
- Harin da ake zargin masu alaƙa da Boko Haram ne suka kai ya kashe sama da mutum 200, ya lalata gidaje da kasuwanni tare da tilasta mazauna tserewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Gwamnatin Kwara ta fitar da sanarwa game da wasu mutane har 176 da aka sace tun a watan Faburairun shekarar 2026.
Gwamnatin Kwara ta sanar a ranar Laraba cewa mutane da aka sace yayin harin da aka kai ƙauyukan Woro da Nuku na ƙaramar hukumar Kaiama a ranar 3 ga Fabrairu, 2026, sun dawo cikin 'yanci bayan sun shafe watanni a hannun masu garkuwa.

Source: Facebook
An bayyana hakan ne ta wani saƙo da gwamnatin Kwara ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta tabbatar da cewa mutane 176 da aka yi garkuwa da su a lokacin harin sun samu 'yanci.
Gwamnatin Kwara ta yaba wa Bola Tinubu
A cikin saƙon, gwamnatin ta gode wa Allah tare da yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, jami'an tsaro da duk waɗanda suka taka rawa wajen tabbatar da nasarar kuɓutar da waɗanda aka sace.
An yi garkuwa da mutanen ne lokacin da wasu da ake zargin masu alaƙa da Boko Haram suka kutsa cikin ƙauyukan Woro da Nuku a kan babura, inda suka kai hari na tsawon sa'o'i da dama.
Rahotanni sun ce harin, wanda ake ɗauka a matsayin ɗaya daga cikin mafi muni a tarihin Kwara, ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 200, ya jikkata mutane da dama, ya lalata gidaje da kasuwanni, sannan ya tilasta wa mazauna yankin tserewa.

Source: Original
Kokarin da jami'an sa-kai suka yi
An kuma ruwaito cewa jami'an sa-kai da suka yi ƙoƙarin dakile maharan sun gamu da ƙarfi, yayin da aka ce wasu daga cikinsu sun makale a ofishinsu kafin aka ƙone su.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana cikakkun bayanai kan yadda aka samu kuɓutar da mutanen 176 da aka sace ba, yayin da ake sa ran za a fitar da ƙarin bayani nan gaba.
Yan bindiga sun yi wa mutane 176 barazana
An ji cewa yan uwan aƙalla mutane 176 da ’yan ta’adda suka sace a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara sun sake roƙon gwamnati ta gaggauta kuɓutar da su.
’Yan uwansu sun ce sun tara sama da Naira miliyan 155 domin biyan kuɗin fansa, amma ana zargin masu garkuwar sun ƙi karɓar kuɗin.
An ce ’yan ta’addan sun yi barazanar aurar da matan da suke ganin kyawawa ne tare da kashe sauran waɗanda suke riƙe da su.
Asali: Legit.ng

