Sanata Goje Ya Sha Kaye, Ya Rasa Tikitin APC na Komawa Majalisar Dattawa a 2027

Sanata Goje Ya Sha Kaye, Ya Rasa Tikitin APC na Komawa Majalisar Dattawa a 2027

  • Tsohon gwamnan Gombe, Danjuma Goje ya rasa tikitin jam'iyyar APC na tsayawa takarar Sanatan Gombe ta Tsakiya karo na biyar a zaben 2027
  • DCP Muhammed Ahmed, wanda gwamna Inuwa Yahaya ke goyon baya ne ya samu nasara a zaben fitar da gwanin da aka gudanar ranar Litinin
  • Dan takarar na APC ya ce an gudanar da zaben cikin lumana ba tare da wata matsala ba a kananan hukumomin Gombe ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe, Nigeria - Sanata Muhammad Danjuma Goje ya rasa tikitin jam’iyyar APC na tsayawa takarar Sanatan Gombe ta Tsakiya karo na biyar a zaben 2027.

Hakan ta faru ne bayan ya sha kaye a zaben fitar da gwani da aka gudanar ranar Litinin, in da tsohon mataimakin kwamishinan yan sanda, DCP Mohammed Ahmed (mai ritaya), ya lashe tikitin APC.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya samu tikitin takarar APC a Kano

Danjuma Goje.
Tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje yana gaisawa da abokan aikinsa a zauren Majalisar dattawa Hoto: Mohammed Danjuma Goje
Source: Twitter

Yadda aka jayar da Danjuma Goje

Daily Trust ta ruwaito cewa DCP Mohammed ya samu nasara ne a zaben kai tsaye da aka gudanar a kananan hukumomin Akko da Yamaltu/Deba.

Da yake bayyana sakamakon, shugaban kwamitin zaben fitar da gwanin, Dr. Habu Dahiru, ya ce DCP Mohammed Ahmed ya samu kuri’u 42,785 yayin da Sanata Goje ya samu kuri’u 10,425.

Tun da farko dai an zabi Ahmed a matsayin dan takarar masalaha na APC a mazabar Sanatan Gombe ta Tsakiya, amma Danjuma Goje ya nuna bai yarda ba.

Sanata Goje ya shafe shekaru yana wakiltar mazabar tun daga shekarar 2011 bayan kammala wa’adinsa biyu a matsayin gwamnan jihar Gombe.

Dan takarar APC ya yi jawabin godiya

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaben, DCP Mohammed ya ce an gudanar da zaben cikin lumana ba tare da wata matsala ba, yana mai cewa yanayin da aka gani ya nuna yadda jama’a ke son sauyi a yankin.

Kara karanta wannan

APC ta hana 'yan siyasa 47 shiga takarar sanata, ta saki cikakken jerin sunayen

Ya ce mambobin jam’iyya da mazauna yankin sun nuna farin ciki da yiwuwar samun wakilci mai karfi a Majalisar Tarayya.

“Kun ga yadda jama’a suke cikin farin ciki. Mutane da yawa sun yi imanin cewa lokaci ya yi da Yamaltu-Deba za ta samu murya mai karfi a matakin kasa,” in ji shi.

Dan takarar APC din ya kara da cewa burinsa ba wai don hana wani damar tsayawa takara ba ne, “amma saboda bukatar jama’a na samun sabon shugabanci.”

Lokacin da aka tuntubi daya daga cikin hadiman Sanata Goje domin jin martaninsa, ya ce ba zai iya yin magana ba sai ya samu izini daga ubangidansa.

A wani labarin, kun ji cewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262