2027: Kakakin Majalisar Kwara Ya Raba Gardama a Zaben Fitar da Dan Takarar Gwamnan APC

2027: Kakakin Majalisar Kwara Ya Raba Gardama a Zaben Fitar da Dan Takarar Gwamnan APC

  • Rt. Hon Salihu Yakubu Danladi ya samu nasarar zama 'dan takarar gwamnan jihar Kwara a inuwar APC a babban zaben 2027
  • Kakakin Majalisar dokokin Kwara ya lashe tikitin APC ne a zaben fitar da gwani da aka gudanar yau Juma'a, 22 ga watan Mayu, 2026
  • Hakan na zuwa ne bayan kwanaki ana kai ruwa rana da lissafin siyasa a cikin jam’iyya mai mulki kan wanda zai gaji Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara, Nigeria - Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Rt. Hon Salihu Yakubu Danladi, ya lashe tikitin takarar gwamna na APC a jihar bayan nasara da ya samu a zaɓen fitar da gwani.

Danladi ya kayar da sauran masu neman takara 14, ciki har da wani sanata mai ci, a zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomi 16 na jihar Kwara, inda ya samu ƙuri’u 94,990.

Kara karanta wannan

Bayan kai ruwa rana, jam'iyyar APC ta tsaida 'dan takarar gwamnan Yobe a zaben 2027

Salihu Yakubu Danladi.
Shugaban majalisar dokokin jihar Kwara, Rt. Hon. Salihu Yakubu Danladi Hoto: Woruyo Abdulmalik
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kwamitin fitar da gwanin APC kuma tsohon ƙaramin ministan tsaro, Musiliu Obanikoro, ne ya sanar da sakamakon a Banquet Hall da ke Ilorin.

APC ta tsaida dan takarar gwamnan Kwara

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Obanikoro ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana da nasara, yana mai cewa babu wanda ya yi rashin nasara a APC.

Ya ce:

“Babu wanda ya yi rashin nasara a kowace gasa ta APC. Dukkanmu masu nasara ne.”

Daga nan ya ayyana Rt. Hon Salihu Yakubu Danladi a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan cika dukkan sharuddan jam’iyyar, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Yadda aka kai ruwa rana a APC

Zaɓen fitar da gwanin ya biyo bayan kwanaki na takun-saka da lissafin siyasa a cikin jam’iyya mai mulki kan wanda zai gaji Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq a shekarar 2027.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce bayan an samu rahotannin da suka bayyana cewa gwamnan ya nuna goyon baya ga Ambasada Yahaya Seriki a matsayin wanda yake so ya gaje shi.

Kara karanta wannan

Gwanna Alia ya tika mutum 2 da kasa, ya lashe tikitin takarar gwamnan APC a zaben 2027

Wannan rahoto dai ya haddasa rashin jin daɗi da suka daga wasu masu neman takara da ƙungiyoyin siyasa a cikin APC.

Rikicin ya ƙara tsananta ne bayan APC ta dakatar da zaɓen fitar da gwani ana tsakiyar kada kuri'a ranar Alhamis, tana mai danganta hakan da matsaloli da dabarun gudanarwa da buƙatar ƙarin tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki.

Salihu Yakubu Danladi.
Kakakin Majalisar dokokin jihar Kwara, Rt. Hon. Salihu Yakubu Danladi tare da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq Hoto: AbdulRahman AbdulRazaq
Source: Facebook

Magoya bayan Danladi sun fara murna

Kafin sake gudanar da zaɓen, Obanikoro ya gana da masu neman takara a sakatariyar APC ta jihar da ke Ilorin, inda ya tabbatar da cewa za a gudanar da sahihin zaɓe cikin gaskiya da adalci.

Magoya bayan Danladi sun barke da murna jim kaɗan bayan sanar da sakamakon, yayin da shugabannin jam’iyyar suka fara ƙoƙarin haɗa kan mambobi domin tunkarar zaɓen gwamna na 2027.

Malam Wali ya lashe tikitin APC a Yobe

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta ayyana tsohon sakataren gwamnatin jihar Yobe, Baba Malam Wali a matsayin dan takarar gwamna a zaben 2027.

An ayyana Malam Wali mai shekaru 68 a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na gwamna da aka gudanar a fadin kananan hukumomin Yobe.

Yobe na daya daga cikin jihohin da aka kai ruwa rana tsakanin masu neman takarar gwamna bayan zaman sulhun da aka gudanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262