Akwai Ladar N60m: Sojoji Sun Saki Hotuna da Bayanan 'Yan Ta'adda 2 da Ake Nema

Akwai Ladar N60m: Sojoji Sun Saki Hotuna da Bayanan 'Yan Ta'adda 2 da Ake Nema

  • Rundunar sojin Najeriya ta ayyana shugaban ISWAP, Abu Musa Shuwa, da mataimakinsa a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo
  • Sojoji sun ce bayanan shugabannin sun fito ne bayan binciken na'urorin da aka ƙwato a hare-haren da aka kai kan ƴan ta'addan ISWAP
  • Rundunar ta yi alƙawarin ba da tukuicin kuɗi ga duk wanda bayanansa suka kai ga kama Abu Musa, tare da kare sirrin masu ba da bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Borno - Rundunar sojin Najeriya ta ayyana shugaban ƙungiyar ISWAP, Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa, da mataimakinsa, Amirul Jaish Muhammad Jidda, a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo.

Wannan kuwa na zuwa ne bayan sojoji sun samun bayanan shugabannin 'yan ta'addar daga na'urorin da aka ƙwato a wani farmaki da aka kai yankin Tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

A ba su wuta: Gwamnan Bauchi ya umarci sojoji a shafe 'yan bindiga

Sojoji sun saki hotunan 'yan ta'addan ISWAP 2 da suke nema ruwa a jallo.
Shugaban sojojin kasan Najeriya, Janar Waidi Shaibu (hagu) da hoton Amirul Jaish da ake nema ruwa a jallo. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

An gano shugabannin ISWAP

Mai riƙon muƙamin jami'in yaɗa labarai na rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Muhammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, in ji rahoton Punch.

Ya ce an gano bayanan shugabannin ne bayan binciken ƙwararru da aka yi kan na'urorin fasaha da sauran muhimman kayayyakin bayanan sirri da aka ƙwato daga ƴan ta'addan.

A cewar Goni, sojoji sun samu nasarar ƙwato na'urar daukar bidiyo da ƴan ISWAP ke amfani da ita wajen ɗaukar bidiyon farfaganda da kuma rubuta ayyukansu.

Binciken da aka gudanar kan na'urorin ya taimaka wajen gano wuraren da ƴan ta'addan ke gudanar da ayyukansu tare da gano sunayen wasu manyan jagororinsu.

Ayyukan 'yan ta'adda a Borno

An ce jagororin suna aiki ne a yankunan Mangari, Metele da Dogon Chukun da ke ƙasan Tafkin Chadi, a ƙananan hukumomin Abadam da Kukawa na jihar Borno.

Daga cikin waɗanda aka gano akwai Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa, mataimakinsa Muhammad Jidda wanda aka fi sani da "Mutumin da ke da hannu ɗaya", da kuma Hamad Abu Hanifa, wanda ke riƙe da muƙamin Amirul-Fiya na ISWAP.

Kara karanta wannan

Dara ta ci gida: Wani bam ya fashe da ƴan ƙungiyar ISWAP yayin da suke hada shi

Rundunar ta bayyana cewa Abu Musa shi ne shugaban ƴan ta'addan da ake nema ruwa a jallo fiye da kowa a yankin Tafkin Chadi.

An sanya ladar kudi ga jama'a

Ta ce za ta ba da tukuicin kuɗi mai tsoka ga duk wanda sahihan bayanansa suka kai ga kama shi, tare da tabbatar da cewa za a kare sirrin masu ba da bayanai bisa ƙa'idojin tsaro.

Sojojin Najeriya na ci gaba da farautar 'yan ta'addan ISWAP
Wasu daga cikin hotunan 'yan ta'addan ISWAP da sojoji ke nema ruwa a jallo. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojojin sun buƙaci al'umma su ci gaba da bai wa jami'an tsaro haɗin kai ta hanyar ba da sahihan bayanai kan motsin waɗanda ake zargi.

Haka kuma sun gargaɗi jama'a da kada su yi yunƙurin kama ko tunkarar waɗanda ake nema, sai dai su kai rahoto ta hanyoyin da jami'an tsaro suka tanada ko kuma ta lambar waya 0708 498 8859.

Sanarwar ta kuma tuna cewa tuni an sanya tukuicin Naira miliyan 50 kan Ibn Muhammad, kwamandan sashen Amniyya na ISWAP, yayin da aka sanya tukuicin Naira miliyan 10 kan Muhammad Jidda.

Sojan da ake nema ya shiga hannu

A wani labari, mun ruwaito cewa, sojoji sun samu nasarar cafke wani jami'in rundunar da ake zargi ya na mu'amala da yan ta'adda tare da sayar masu da makamai ana kai hare-hare.

Kara karanta wannan

Bayani kan ƙarin albashi da Tinubu ya yi wa ƙanana da manyan sojojin Najeriya

Sojojin sun kama jami'in mai suna Mohammed Yusuf a Maiduguri yayin da ake zarginsa da ƙoƙarin tserewa zuwa wata kasar domin gujewa hukuma.

Rundunar Sojin Najeriya ta ce bincike na ci gaba domin gano cikakken girman abin da ya aikata da kuma duk wanda ya taimaka masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com