Gwamna Ya Yanke Hukunci, Ya Yi Wa Shugaba Tinubu Alkawarin 95% na Kuri'u a Zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
- Gwamna Uba Sani ya sha alwashin bai wa Shugaba Bola Tinubu akalla kashi 95% na kuri'un mutanen Kaduna a zaben 2027
- Gwamnan ya yabawa Tinubu kan ayyukan raya kasa da ake aiwatarwa a Arewacin Najeriya, yana mai cewa an riga an kammala zabe mai zuwa
- Malam Uba Sani ya ce babu wani shugaban Najeriya da ya yi wa Arewa ayyukan ci gaba kamar Tinubu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumar nasara a jihar a zaben shekarar 2027.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne ranar Talata yayin kaddamar da aikin gina titin Kaduna zuwa Birnin Gwari mai tsawon kilomita 122.

Source: Facebook
A rahoton Vangaurd, Uba Sani ya kuma yabawa shugaban kasa kan abin da ya bayyana a matsayin gagarumin zuba jari a Arewacin Najeriya.
"Kaduna ita ce zuciyar Arewa"
Uba Sani ya ce jihar Kaduna na da muhimmanci ta fuskar siyasa da tattalin arziki a Arewacin Najeriya, yana mai cewa ci gaban jihar na amfani ne ga daukacin yankin.
Ya ce:
"Ina tabbatar muku Kaduna ita ce babban birnin Arewacin Najeriya. Kowa yana alfahari da Kaduna. Ci gaban Kaduna ci gaba ne ga dukkan jihohin Arewa, ko muna so ko ba ma so."
Ya yi alkawarin marawa Tinubu baya
Gwamnan ya gode wa Shugaba Tinubu bisa fahimtar muhimmancin Kaduna, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba shi cikakken goyon baya.
Uba Sani Y'ya ce:
"Za mu ci gaba da nuna goyon bayanmu. Za mu ci gaba da marawa shugaban kasa baya."
An ware wa Tinubu 95% na kuri'un Kaduna
Uba Sani ya ce yana da yakinin cewa Tinubu zai samu akalla kashi 95 cikin 100 na kuri'un da za a kada a Kaduna.
A cewarsa:
"Ba ni da wata shakka cewa an riga an kammala zaben 2027. Ba ni da wata shakka cewa za mu ba shugaban kasa akalla kashi 95 cikin 100 na kuri'un Kaduna. Duk wanda bai yarda ba, ina shirye ya kalubalance ni."

Source: Twitter
Ya yabawa Tinubu kan ayyukan Arewa
Gwamnan ya sake nanata matsayinsa na baya cewa babu wani shugaban Najeriya da ya aiwatar da ayyukan ci gaba a Arewacin kasar kamar Shugaba Tinubu.
Ya ce kimanin watanni biyu da suka gabata ya bayyana hakan a fili, kuma har yanzu babu wanda ya gabatar da hujjar da ta saba da wannan ikirari.
Ya kara da cewa ayyukan da ake gudanarwa a sassa daban-daban na Arewa sun nuna irin kudirin shugaban kasa na bunkasa yankin, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Uba Sani ya zabi mataimaki kirista
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Uba Sani ya bayyana Kirista, Jerry Adams, a matsayin mataimakinsa a zaben gwamnan Kaduna na 2027.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce ya dauki matakin ne bayan gudanar da tuntuba da dama, nazari mai zurfi da kuma addu'o'i.
Asali: Legit.ng

