Gwamna Buni da 'Yan APC Sun Fitar da Dan Takarar Gwamnan Yobe a 2027

Gwamna Buni da 'Yan APC Sun Fitar da Dan Takarar Gwamnan Yobe a 2027

  • Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Yobe sun bayyana wanda suke so ya tsaya masu takarar gwamna a zaben 2027 da ke tafe
  • Rahotanni sun nuna cewa sun bayyana matsayarsu ne yayin wani zama da suka yi a birnin tarayya Abuja tare da gwamna Mai Mala Buni
  • Gwamnatin jihar Yobe ta bayyana dalilan zaban Baba Malam Wali a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar APC takara a zabe mai zuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe - Kungiyar masu ruwa da tsaki ta jam’iyyar APC a Jihar Yobe ta bayyana goyon bayanta ga tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Baba Malam Wali, a matsayin wanda take so ya zama dan takarar gwamna a zaben 2027.

An bayyana hakan ne cikin wata sanarwar bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilun 2026 a Abuja.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Peter Obi ya bayyana dalilin ganawa da Jonathan

Wanda aka zaba ya yi wa APC takara a Yobe a 2027
Gwamna Mai Mala Buni ya daga hannun Baba Malam Wali. Hoto: Mamman Muhammed
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da yadda aka zabi Baba Malam Wali ne a wani sako da mai magana da yawun Mai Mala Buni, Mamman Muhammad ya fitar a Facebook.

Wanda zai yi wa APC takara a Yobe

Kungiyar ta bayyana Wali a matsayin gogagge kuma kwararre, wanda ya cancanta, mai hakuri da kuma halayen da suka dace don shugabanci nagari da gudanar da mulki.

Ta kuma jaddada cewa dogon lokacin da ya yi yana aiki a gwamnatoci daban-daban a jihar ya ba shi damar fahimtar yanayin Yobe, tare da cancantar ci gaba da gina manufofi da tsare-tsaren da aka fara.

Masu ruwa da tsakin sun ce gogewarsa a harkokin gwamnati ne yasa sua ga ya dace ya ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shirye masu kyau a Jihar Yobe.

Sanarwar ta kunshi cewa:

"Kungiyar ta tabbatar da Baba Malam Wali a matsayin zabin ta na takarar gwamna a 2027, bayan taron da aka yi a Abuja."

Kara karanta wannan

Kwamishinan Ganduje ya amsa kiran masoya Tinubu, zai nemi kujerar sanata a Kano

Hakan na zuwa ne bayan kungiyar ta ce jam’iyyar ta amince da amfani da tsarin sulhu wajen fitar da ‘yan takara a zabuka masu zuwa.

Gwamna Mai Mala Buni da 'yan APC
Masu ruwa da tsakin APC a Yobe bayan taron da suka yi a Abuja. Hoto: Mamman Muhammad
Source: Facebook

APC a Yobe ta amince da Tinubu

Punch ta wallafa cewa kungiyar jam’iyyar APC a jihar Yobe ta amince da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben 2027.

Gwamnan jihar, Mai Mala Buni, da kuma shugaban kungiyar masu ruwa da tsaki na jihar, Sanata Ibrahim Gaidam, sun ce jam’iyyar za ta ci gaba da tattaunawa domin karfafa hadin kai a cikinta.

An zabi dan takarar APC a Legas

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya amince da mataimakinsa ya tsaya takarar gwamna a 2027.

Babajide Sanwo-Olu ya bayyana haka ne bayan wani zama da musamman da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a gidan gwamnati.

Shugabannin APC da masu ruwa da tsaki a jihar sun bayyana cewa sun amince da kwarin gwiwar mataimakin gwamnan, Dr. Kadri Obafemi Hamzat.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng