Gwamna Buni Ya Fadi Matsayar APC kan Zaben Fitar da Gwani a Yobe
- Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi tsokaci kan batun fitar da 'yan takara a jihar domin zaben shekarar 2027
- Mai Mala Buni ya bayyana cewa jam'iyyar APC a shirye take ta gudanar da zaben fitar da gwani domin zabar 'yan takara
- Kalaman gwamnan na zuwa ne a matsayin martani kan cece-kucen da ake yi kan tsayar da dan takarar gwamnan jihar ta hanyar maslaha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana cewa jam’iyyar APC a jihar a shirye take ta gudanar da zaɓen fitar da gwani na adalci kuma sahihi.
Mai Mala Buni ya ce za a gudanar da zaben fitar da gwanin ne idan har ƙoƙarin samar da ’yan takara ta hanyar maslaha bai yi nasara ba gabanin babban zaɓen 2027.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce Buni ya bayyana hakan ne yayin mayar da martani ga damuwar da ake nunawa game da zaɓar tsohon sakataren gwamnatin jiha, Baba Mallam Wali, a matsayin wanda jam’iyyar ta fi so ya zama ɗan takarar gwamna.
Meyasa aka zabi Wali?
A cewar gwamnan, zabar Wali ta biyo bayan ƙudurin da aka cimma a wani taro na manyan masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar 23 ga watan Afrilu, 2026.
“Zabar Baba Mallam Wali a matsayin wanda jam’iyyar ta fi so ya biyo bayan ƙudurorin taron manyan masu ruwa da tsaki na ranar 23 ga Afrilu, 2026. An amince da shi kuma aka zabe shi a matsayin wanda ake so, amma idan ba a samu matsaya ɗaya ba, za mu ɗauki tsarin zaɓe."
- Mai Mala Buni
Buni ya ce za a yi zaben fitar da gwani
Gwamnan ya lura cewa jam’iyyar ba ta yi watsi da tsarin zaɓen fitar da gwani na kato bayan kato ba domin samar da ’yan takara na muƙaman zaɓe daban-daban a jihar.
“Wannan ba sabon abu ba ne. A shekarar 2019, an zaɓe ni a matsayin ɗan takarar maslaha, wasu ’yan takara kaɗan suka ƙalubalanci shawarar, muka tafi zaɓe inda na fito a matsayin ɗan takarar jam’iyya da tazara mai faɗi. Muna shirye mu maimaita wannan tarihin idan ba mu cimma matsaya ta maslaha ba."
- Mai Mala Buni
Buni ya bayyana cewa shugabancin jam’iyyar yana ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma masu neman takara domin tabbatar da an warware maganar cikin lumana.
“Muna tattaunawa da juna kuma muna tuntuɓar masu ruwa da tsaki, har da masu neman takara, domin cimma maslaha ta cikin gida."
- Mai Mala Buni
Gwamna Buni ya bukaci hadin kai
Gwamnan ya jaddada cewa haɗin kai a cikin jam’iyyar shi ne babban abin da ya sa a gaba, yana mai cewa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin mambobin APC ya zama dole domin nasarar jam’iyyar a zaɓubbukan 2027, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
“A matsayina na gwamnan jiha, zan kasance mutumin da ya fi kowa farin ciki idan na ga jihar da jam’iyya suna cikin zaman lafiya da haɗin kai. Mu mazauna jihar Yobe ne kuma mambobin APC. Burina shi ne na ga mun ƙara haɗa kai kuma muna aiki tare don ganin ’yan takararmu sun yi nasara a babban zaɓen 2027."

Kara karanta wannan
ADC ta fadi hanyar da za ta zabi dan takarar shugaban kasa bayan ficewar Kwankwaso da Obi
- Mai Mala Buni

Source: Facebook
Ya tabbatar wa mambobin jam’iyyar cewa za a tafi da kowa da kowa ba tare da la’akari da wanda ya fito a matsayin ɗan takarar APC ba a ƙarshe.
Haka kuma, Buni ya yi kira ga mambobin APC a faɗin jihar da su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai tare da tara wa jam’iyyar goyon baya gabanin zaɓubbukan 2027.
Tsohon IGP ya shiga takarar gwamnan Yobe
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sufeta janar na 'yan sanda, Usman Baba Alkali, ya shiga takarar gwamnan jihar Yobe.
Majiyoyi sun ce tsohon shugaban 'yan sandan ya shiga tafiyar ce bayan shirin samar da ɗan takarar sasanci tsakanin masu neman kujera ya rushe.
Alkali ya ce wasu ‘yan takara huɗu sun riga sun karɓi fom ɗin tsayawa takara, abin da ya tabbatar masa cewa yarjejeniyar sasanci tsakanin masu neman kujerar ta lalace gaba ɗaya.
Asali: Legit.ng

