Sanata Zai Rikita APC, Ya Yi Watsi da Sakamakon Zaɓen Fitar da Gwani a Cross River

Sanata Zai Rikita APC, Ya Yi Watsi da Sakamakon Zaɓen Fitar da Gwani a Cross River

  • Sanatan a majalisar dattawan Najeriya Eteng Williams ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen fitar da gwani na APC a Cross River ta Tsakiya
  • 'Dan majalisar ya kafe a kan cewa babu wani zaɓe da aka gudanar a mazaɓu 66 na yankin, saboda haka ba zai amince da sakamako ba
  • Eteng Williams ya buƙaci shugabannin APC na ƙasa su binciki yadda aka gudanar da tsarin domin kare mutuncin jam’iyyar gabanin 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Cross River – Sanatan da ke wakiltar Cross River ta Tsakiya a majalisar dattawa, Eteng Williams, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC da aka ce an gudanar a yankinsa.

Sanatan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Calabar ranar Talata, 19 ga watan Mayu, 2026.

Kara karanta wannan

Duk da ƙaryata Amurka, an tabbatar da hannun Trump a hallaka jagoran ISIS a Najeriya

Sanata Eteng Williams ya yi fatali da zaben APC
Sanata Eteng Williams a zaune a Majalisar dattawa Hoto: Senator Eteng Jonah Williams
Source: Facebook

A ruwayar Premium Times, Sanatan ya ce babu wani zaɓe da aka gudanar a ko ɗaya daga cikin mazaɓu 66 na yankin sanatan, yana mai cewa duk wani sakamako da ake yaɗawa ba shi da tushe balle makama.

Zaben tsaida gwani ya fusata Sanatan APC

Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa Eteng Williams ya ce shi da magoya bayansa sun zagaya dukkannin yankin domin tabbatar da yadda zaɓen ke gudana, amma ba su ga jami’an jam’iyya ko kayan gudanar da zaɓe ba.

A kalamansa:

“Ba a yi zaɓe a mazaɓu 66 na yankin nan ba. Mun zagaya dukkannin yankin domin ganin yadda ake gudanar da zaɓen."
Williams ya ce babu inda aka yi zaben fitar da gwani a Cross River
Sanata Eteng Williams a yayin wani taro tare da mai ba shi tsaro Hoto: Senator Eteng Jonah Williams
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa sun jira har wajen 8:00 na dare domin su kaɗa ƙuri’unsu, amma babu jami’an da suka bayyana domin gudanar da aikin.

Ya kara da cewa:

“Idan babu jami’ai kuma ba a gudanar da zaɓe ba, ta yaya aka samu sakamako?”

Kara karanta wannan

2027: Martanin Kwankwaso ga zargin yana yi wa Tinubu aiki a NDC

Sanata ya nemi daukin APC ta kasa

Sanatan ya buƙaci shugabannin APC na ƙasa su duba yadda aka gudanar da tsarin cikin adalci da kishin dimokuraɗiyyar cikin gida.

Haka kuma ya roƙi magoya bayan jam’iyyar da su yi watsi da rahotannin da ke cewa an bayyana wani mutum a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Ya bayyana cewa zaɓe wata dama ce da ‘yan siyasa ke amfani da ita domin gwada farin jininsu a wajen jama’a, yana mai zargin cewa wasu mutane na son samun shugabanci ta “ƙofar baya.”

Sanatan ya ce:

“Muna ganin tsananin kwaɗayi ne kawai. Wasu suna son zama shugabanni ta hanyar da ba ta dace ba."

Sanatan ya kuma ce babu wani jami’in jam’iyya da ya tuntube shi domin ya tura wakilansa yayin gudanar da zaɓen fitar da gwani. Ya jaddada cewa jam’iyyar APC na buƙatar yin abin da ya dace domin kare martabarta da mutuncinta a idon jama’a.

Tsohon gwamna, Sanata Goje ya sha kaye

Kara karanta wannan

Hankalin Wike ya tashi da gwamnan Oyo ya fito zai kara da Tinubu a 2027

A baya, mun kawo labarin cewa tsohon gwamnan Gombe, Danjuma Goje ya rasa tikitin jam'iyyar APC na tsayawa takarar Sanatan Gombe ta Tsakiya karo na biyar a zaben 2027 mai zuwa.

DCP Muhammed Ahmed, wanda gwamna Inuwa Yahaya ke goyon baya ne ya samu nasara a zaben fitar da gwanin da aka gudanar ranar Litinin 18 ga watan Mayu, 2026 don neman kujerar da Goje ke kai.

'Dan takarar na APC ya ce an gudanar da zaben cikin lumana ba tare da wata matsala ba a kananan hukumomin yankin Gombe ta Tsakiya kafin a sanar da rashin nasararsa na neman koma wa majalisa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng