Rikici a APC: Sanata Mai Ci Ya Yaki Amince wa da Sakamakon Zaben Fitar da Gwani
- Sanata Ned Nwoko ya yi zargin cewa an tafka magudi, sayen kuri’u da tsoratar da masu kada kuri’a a zaben fitar da gwani na APC
- Tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, ya lashe zaben a cewar APC, amma Nwoko ya ce shi ne ya samu rinjayen kuri’u a zaben
- Nwoko ya bukaci shugabannin APC su binciki yadda aka gudanar da zaben fitar da gwani na mazabarsa ta Delta ta Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Sanatan da ke wakiltar Delta ta Arewa a majalisar dattawa, Ned Nwoko, ya yi watsi da sakamakon zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC.
Sanata Ned Nwoko ya zargi masu shirya zaben da aikata magudi, sayen kuri’u da kuma tsoratar da masu kada kuri’a.

Source: Twitter
An bayyana matsayar tasa ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a, inda Chris Okobah ya wakilce shi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan
"Har da talauci a ciki," Ministan Yar'Adua ya fadi dalilin shiga takarar gwamna a Akwa Ibom
Sanata Nwoko ya ce shi ya lashe zabe
Okobah ya ce Sanata Ned Nwoko ne ya yi nasara a zaben da babban rinjaye, inda ya kayar da tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa.
A cewarsa, alkaluman da suke da su sun nuna cewa Nwoko ya samu kuri’u 123,000 yayin da Okowa ya samu kuri’u 5,000 kacal.
Ya ce suna da hujjoji daga mazabu daban-daban da ke tabbatar da sakamakon da suke ikirari.
“Akwai mazabu 98 kuma muna da bidiyo, rahotannin wakilai da bayanan matakin mazabu da ke nuna abin da ya faru a daukacin yankin sanatan,” in ji Okobah.
“An fara magudi tun kafin zabe”
Chris Okobah ya yi ikirarin cewa tun kafin ranar gudanar da zaben fitar da gwanin ne aka shirya magudin, kuma har a ranar zaben ma an yi hakan.
A cewarsa, an hana Sanata Ned Nwoko damar ganawa da kwamitin gudanar da zaben da aka ajiye a gidajen gwamnati na musamman, in ji rahoton The Guardian.
Ya zargi wasu manyan masu ruwa da tsaki a jihar da sarrafa kwamitin zaben tare da nada jami’an tattara sakamako daga cikin kwamishinoni da masu ba gwamnati shawara.
Zargin sayen kuri'u a zaben APC
A cewar wakilin sanatan, babu sahihiyar hanyar tantance masu kada kuri’a, babu gaskiya a kirga kuri’u kuma ba a tattara sakamakon zaben bisa adalci ba.
“An rubuta sakamako tun a daren ranar zaben, tun ma kafin mutane su fito su kada kuri’arsu," In ji Chris Okobah.
Okobah ya kuma bayyana cewa sun samu rahotanni kan sayen kuri’u da raba kudade ga masu kada kuri’a da jami’an jam’iyya domin murde ra’ayin jama’a.
Sanata Ned Nwoko ya ce ba zai hakura ba wajen kare abin da ya kira zabin jama’a, tare da bukatar shugabannin APC su gudanar da bincike mai zurfi kan yadda aka gudanar da zaben.
Asali: Legit.ng
