APC: Akpabio, Barau Jibrin da Gwamnoni 7 Za Su Fafata Neman Takarar Sanata Yau
- Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da gwamnoni bakwai na daga cikin manyan ‘yan siyasar da ke neman tikitin sanata a APC
- Akwai tsofaffin gwamnoni irin su Yahaya Bello, Simon Lalong da Jolly Nyame da suka shiga fafatawar kujerun sanata a jihohinsu
- Tsohon gwamnan Ogun, Gbenga Daniel, ya janye daga zaben fitar da gwani yayin da yake zargin akwai shirin tayar da rikici a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Manyan jiga-jigan siyasa a Najeriya sun shiga zaben fitar da gwani na kujerun sanata da jam’iyyar APC ke gudanarwa a yau Litinin domin shirye-shiryen zaben 2027.
Daga cikin manyan ‘yan siyasar da ake sa ran za su fafata akwai shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da mataimakinsa, Barau Jibrin.

Source: Facebook
Gwamnoni masu neman kujerar Sanata
Sauran manyan 'yan siyasar sun hada da shugaban masu rinjaye, Opeyemi Bamidele da bulalar majalisar, Mohammed Tahir Monguno, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Haka kuma gwamnoni bakwai masu ci sun shiga neman tikitin sanata a karkashin APC bayan kammala wa’adinsu.
Gwamnonin da suka shiga takarar sun hada da Hope Uzodimma na jihar Imo, Ahmadu Fintiri na Adamawa, Abdullahi Sule na Nasarawa da Mai Mala Buni na Yobe.
Sauran sun hada da AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara, Muhammadu Inuwa Yahaya na Gombe da Dapo Abiodun na Ogun.
Tsofaffin gwamnoni sun shiga fafatawa
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa tsofaffin gwamnoni da dama su ma sun shiga zaben fitar da gwani na sanata a APC.
Daga ciki akwai Yahaya Bello na jihar Kogi, wanda ake sa ran zai kara da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta PDP idan ya samu tikitin jam’iyyarsa.
Hakazalika tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, wanda yanzu Sanata ne, zai sake neman kujerarsa a yayin da Gwamna Inuwa Yahaya ke neman karbe kujerar.
Sauran tsofaffin gwamnoni da ke neman kujerar Sanata sun hada da Jolly Nyame na Taraba, Simon Lalong na Plateau da Danjuma Goje na Gombe.

Kara karanta wannan
"Dama sharrin shaidan ne": Abba ya kawo ƙarshen rikicin Rurum da Kawu Sumaila a Kano
APC ta kafa kwamitocin sauraron korafi
Jam’iyyar APC ta fara gudanar da zabukan fitar da gwani tun ranar Asabar da zabukan ‘yan takarar majalisar wakilai.
Jam’iyyar ta kuma kafa kwamitocin sauraron korafe-korafe a jihohi daban-daban domin duba koke-koken da za su iya tasowa bayan zabukan.
Mai magana da yawun APC na kasa, Felix Morka, ya bukaci mambobin kwamitocin su kasance masu adalci da gaskiya yayin gudanar da aikinsu.

Source: Twitter
Gbenga Daniel ya janye daga takara
A wani bangaren kuma, tsohon gwamnan Ogun kuma Sanata mai wakiltar Ogun ta Gabas, Gbenga Daniel, ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na APC.
Daniel ya zargi cewa akwai shirin tayar da rikici da kai hari ga magoya bayansa a jihar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ana ganin matakin ya samo asali ne daga rikicin siyasa tsakaninsa da gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, kan tikitin sanata na Ogun ta Gabas.
Shugaban majalisa ya fadi zaben APC
A wani labari, mun ruwaito cewa, shugaban majalisar Nasarawa, Danladi Jatau, ya sha kaye a takarar kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya a zaben fitar da gwani na APC.
Wasu ‘yan majalisar wakilai biyu masu ci sun rasa tikitin komawa takara a zabukan fitar da gwani da aka gudanar a jihar gabanin zaben 2027.
Kwamitin APC ya bayyana zaben a matsayin wanda aka gudanar cikin lumana, adalci da gaskiya a dukkannin kananan hukumomi 13 na Nasarawa.
Asali: Legit.ng

