Yadda Aka Fi Ƙarfin Gwamnan Kwara kan Tsayar da Magajinsa, Aka Zaɓi Kakakin Majalisa
- Kakakin majalisar dokokin Kwara, Salihu Yakubu Danladi, ya lashe tikitin gwamna na APC bayan rikicin cikin gida a jihar
- Gwamna Abdul Rahman AbdulRazaq ya fara goyon bayan Yahaya Seriki, amma matsin lamba daga manyan jam’iyya ya sauya tunani
- Bayan dage zaben fitar da gwani saboda sabani, Danladi ya samu cikakken goyon baya daga gwamnati sannan ya doke sauran ‘yan takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Kakakin majalisar dokokin Kwara, Rt. Hon. Salihu Yakubu Danladi, ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar APC.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa kakakin majalisar ya samu nasara ne bayan zaben fitar da gwani mai cike da rikice-rikice da siyasa.

Source: Facebook
Kuri'un da kakakin majalisar Kwara ya samu
Danladi ya samu kuri’u 94,990 wanda ya zarce kashi 65 cikin 100, inda ya kayar da sauran ‘yan takara 14 a dukkan kananan hukumomi 16, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan
2027: Kakakin majalisar Kwara ya raba gardama a zaben fitar da dan takarar gwamnan APC
Babban abokin hamayyarsa, Ambasada Abdulfatai Yahaya Seriki, ya samu kuri’u 41,700 yayin da tsohon shugaban APC na Kwara, Bashir Omolaja Bolarinwa, ya samu 22,118.
Shugaban kwamitin zaben fitar da gwani na APC, Sanata Musiliu Obanikoro, ne ya sanar da sakamakon a sakatariyar jam’iyyar APC da ke Ilorin ranar Juma’a.
Bayyanar Danladi a matsayin wanda ya lashe zaben ta biyo bayan makonni na rikicin siyasa tsakanin manyan APC kan wanda zai gaji gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.
Tun farko rikicin siyasar ya fi karkata tsakanin Ambasada Yahaya Seriki da Sanata Saliu Mustapha kafin daga baya siyasar ta sauya akala sosai.
Gwamna AbdulRazaq ya fito fili ya bayyana Yahaya Seriki a matsayin wanda yake so ya gaje shi bayan tuntuba da shugabanni da masu ruwa da tsaki.

Source: Facebook
Yadda aka juya akalar zaben fitar da gwani
Majiyoyin jam’iyya sun bayyana cewa matsin lamba daga bangarori daban-daban ya hana aiwatar da wata yarjejeniya da aka shirya tun farko cikin APC.
Kungiyoyi daga yankin Kwara ta Kudu sun yi adawa da ci gaba da rike mulki a Kwara ta Tsakiya tare da neman adalci a siyasar.

Kara karanta wannan
Bayan kai ruwa rana, jam'iyyar APC ta tsaida 'dan takarar gwamnan Yobe a zaben 2027
An dakatar da zaben fitar da gwani na ranar Alhamis 21 ga watan Mayun 2026 saboda matsalolin tsari da kuma ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki cikin APC.
Sai dai majiyoyi sun ce dakatarwar ta samo asali ne daga rashin jituwar manyan bangarorin APC da kuma fargabar karin rabuwar kai.
Kafin sake gudanar da zaben ranar Juma’a, Obanikoro ya gana da ‘yan takara tare da ba su tabbacin gaskiya da adalci a tsarin, cewar Punch.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya fara karkata zuwa yankin Kwara ta Arewa musamman wajen goyon bayan kakakin majalisar jihar Danladi.
An daure kakakin PDP kan taba gwamnan Kwara
Mun ba ku labarin cewa wata babbar kotu da ke zamanta a jihar Kwara ta tura sakataren yada labaran jam'iyyar PDP gidan yari kan zargin bata sunan gwamna.
Alkalin kotu ya ƙi bayar da belin Olusegun Olushola Adewara, saboda rashin bin ƙa’ida wajen gabatar da buƙatar bayan an aika shi gidan maza.
Sai dai jam'iyyar PDP ta fusata da wannan hukunci, inda ake zargin gwamnatin Kwara da amfani da iko wajen murƙushe ‘yan adawan jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng