Babbar Magana: Atiku Ya Yi Gargadi Mai Zafi ga INEC, Tinubu kan Zaben Osun

Babbar Magana: Atiku Ya Yi Gargadi Mai Zafi ga INEC, Tinubu kan Zaben Osun

  • Atiku Abubakar ya gargadi INEC da hukumomin tsaro kan yawaita jami’an tsaro a zaben gwamnan Osun, yana mai cewa zaben gwaji ne ga Najeriya
  • Dan takarar shugaban kasa na ADC ya ce zabe aikin farar hula ne, ba aikin soja ba, yana mai neman a tabbatar da gaskiya da adalci
  • Atiku ya kuma bukaci a fayyace bambance-bambancen da aka ruwaito a takardar shaidar karatun Tinubu da aka gabatar wa INEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya gargadi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), hukumomin tsaro da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Atiku Abubakar ya gargade su kan mayar da zaben gwamnan Osun tamkar aikin soja ko amfani da hukumomin gwamnati domin amfanin jam’iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya tabo maganar raba Najeriya saboda sabani

Atiku ya taso da batun takardun Tinubu
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: @atiku
Source: Twitter

Atiku ya bayyana hakan ne a yayin taron shugabannin matasan ADC na kasa da aka gudanar a Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Me Atiku ya ce kan zaben Osun?

Dan takarar shugaban kasar na ADC ya ce zaben Osun “gwaji ne” ga ikon Najeriya na gudanar da sahihin zabe gabanin babban zaben da ke tafe.

Ya ce yawan jami’an tsaro da yadda aka shirya tura su zuwa wuraren da za a gudanar da zaben na kama da shirye-shiryen yaki maimakon aikin dimokuradiyya na farar hula.

“Zabe aikin farar hula ne, ba aikin soja ba. Kuri’u ba harsasai ba ne. Masu kada kuri’a ba sojojin makiya ba ne. ‘Yan adawa ba ‘yan tawaye ba ne,” in ji shi.

Atiku ya tambayi dalilin da ya sa ba a tura irin wannan dimbin jami’an tsaro wajen yaki da ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga da ke kashe ‘yan Najeriya da kai hare-hare kan al’ummomi ba.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: An tura saƙo ga Amurka da Birtaniya don su hukunta sanatan Najeriya

Atiku ya gargadi INEC

Atiku ya gargadi INEC kan “matsalolin da ba a bayyana dalilinsu ba, jinkirin da ba a yi bayani a kansa ba ko magudi”, yana mai bukatar kayan zabe su isa cikin lokaci, a gudanar da kada kuri’a ba tare da cikas ba, a kirga kuri’u cikin gaskiya sannan a bayyana sakamako cikin tsari na gaskiya.

“‘Yan sandan na Najeriya ne. Sojojin na Najeriya ne. INEC ta al’ummar Najeriya ne. Babu wani daga cikinsu da yake na APC,” in ji shi.
“Duniya na kallon Osun. ‘Yan Najeriya na kallo. Tarihi na rubuta abin da ke faruwa. A bar jama’a su kada kuri’a. A tabbatar da kowace kuri’a. Kuma a bar muradin jama’a ya yi nasara.”

Atiku ya tayar da maganar takardun Tinubu

Atiku ya kuma sake yin tambayoyi kan takardar shaidar karatu daga Chicago State University da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa INEC, yana mai cewa bambance-bambancen da aka gani a takardar na bukatar bayani.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Obi, Kwankwaso sun zauna da yan takarar gwamna 25 a NDC

Ya ce rahotanni sun nuna cewa takardar da aka gabatar wa INEC tana dauke da ranar 22 ga Yuni, 1979, yayin da wata takarda da aka samar dangane da bayanan jami’ar ke dauke da ranar 27 ga Yuni, 1979.

Ya ce an kuma ruwaito cewa akwai bambance-bambance a sa hannun jami’ai da kuma yadda aka bayyana digirin, jaridar The Punch ta kawo rahoton.

Atiku ya tambayi dalilin da ya sa sunaye ko sa hannun jami’an jami’ar da wa’adin aikinsu ya zo shekaru bayan 1979 suka bayyana a kan takardun da ke dauke da wannan shekarar.

Ya kuma tambayi ko an sake samar da wasu takardun shaidar karatu a baya, kuma idan haka ne, wa ya ba da izinin samar da su.

Atiku ya gargadi hukumar INEC
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taron ADC Hoto: @atiku
Source: Twitter

Ortom ba zai goyi bayan Atiku ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa ba shi da wani dalili ko shirin goyon bayan dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar.

Ortom ya jaddada cewa ba zai goyi bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ko wani dan takarar shugaban kasa daga Arewa a babban zaben 2027 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng