Rigima Ta Kunno Kai a Tafiyar Kwankwaso da Peter Obi? An Tsage Gaskiya
- Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun yi martani kan rahotannin rikicin neman madafun iko kan tsarin kwamitin yakin neman zaben NDC na 2027
- Mai magana da yawun Kwankwasiyya ya ce har yanzu ana tuntubar masu ruwa da tsaki kafin fitar da sunayen mambobin kwamitin
- Yunusa Tanko ya ce aikin kwamitin yakin neman zabe ya kamata ya kasance na hidima ga jam'iyya, ba neman biyan buƙatun kashin kai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Bangarorin ɗan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, da mataimakinsa Rabiu Kwankwaso, sun yi martani kan rahotannin samun rikici a tsakaninsu.
Bangarorin na Kwankwaso da Peter Obi sun musanta rahotannin samun rikicin neman madafun iko kan tsarin kwamitin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar na 2027

Source: Facebook
Majiyoyi daga sansanonin ’yan siyasar biyu suka tabbatar da hakan ga jaridar The Punch a wasu tattaunawa daban-daban.
Rahotanni sun ce wasu jiga-jigan jam’iyyar da magoya bayan sansanonin biyu na fafutukar samun muƙamai masu tasiri a kwamitin yakin neman zaɓen, gabanin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a ranar 19 ga watan Agusta.
Kwankwasiyya ta musanta rikicin
Sai dai mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya Movement, Habibu Muhammed, ya bayyana rahoton rikicin a matsayin jita-jita.
Muhammed ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tuntubar jam’iyyar, ɗan takarar shugaban ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki.
“Wannan jita-jita ce. Babu wani rikicin neman madafun iko ko faɗa a ko’ina kan wanda zai kafa kwamitin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na NDC."
Babu rikicin cikin gida
Dr Habibu Mohammed ya kuma jaddada cewa babu wani rikicin cikin gida a jam’iyyar.

Kara karanta wannan
Fitaccen mawaki ya ɗauki abubuwan da ke faruwa a Najeriya ya kai gaban shugaban Amurka
“Ina son in bayyana muku cewa babu wani rikicin cikin gida a NDC dangane da wani tsarin yakin neman zaɓe ko wani abu makamancin haka."
Mohammed ya kuma musanta zargin samun rikici a jam’iyyar, yana cewa babu wata matsala a cikinta kuma babu wanda ke fafutukar samun wani abu.
Ya ce kwamitin sulhu da aka kafa kwanan nan ba shi da alaƙa da rikicin cikin gida, illa dai an kafa shi ne domin magance matsalolin ’yan takarar da suka fafata a zaɓen fidda gwani amma suka sha kaye.
An yi kira ga 'yan NDC
A nasa ɓangaren, Dr Yunusa Tanko, National Coordinator na Obidient Movement Worldwide, ya yi kira da a ɗauki kwamitin yakin neman zaɓe a matsayin wata kafa ta hidima, ba wurin biyan buƙatun kai ba.
"Wasu mutane yanzu ba sa kallon shiga kwamitin yakin neman zaɓe a matsayin kira na yin hidima. Yanzu abin ya koma batun buƙatun kai.
“Mu a Obidient Movement, har yanzu muna kallonsa a matsayin hidima. Idan na cancanci yin hidima a wani wuri, zan yi. Idan ban cancanta ba, zan bar wurin domin wani wanda ya fi ni cancanta ya zo ya yi hidima.” In ji shi
NDC ta musanta fafutukar neman muƙamai
Da aka tuntubi Osa Director, sakataren yaɗa labarai na ƙasa na NDC, shi ma ya musanta rahoton fafutukar neman samun muƙamai.
Ya ce jam’iyyar na tuntubar masu ruwa da tsaki kafin ta bayyana kwamitin yakin neman zaben na ta.

Source: Facebook
Obi, Kwankwaso sun zauna da 'yan takarar NDC
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, tare da abokin takararsa, Rabi’u Kwankwaso, sun gana da manyan ‘yan jam’iyyar.
An gudanar da taron ne domin tattaunawa kan dabarun karfafa tsarin yakin neman zaben jam’iyyar a matakin kasa da jihohi.
Asali: Legit.ng

