APC Ta Sauya Sakamakon Zabe, An Ayyana Yusuf Gagdi a Matsayin Sahihin Ɗan Takara

APC Ta Sauya Sakamakon Zabe, An Ayyana Yusuf Gagdi a Matsayin Sahihin Ɗan Takara

  • Jam’iyyar APC ta soke sakamakon farko da ya bayyana John Tongshinen a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Pankshin/Kanke/Kanam
  • Shugabar kwamitin zaben fitar da gwani na APC, Stella Okotete, ta ce sakamakon farko ba shi da inganci kuma an sanar da shi ba tare da izini ba
  • APC ta ayyana dan majalisar wakilai mai ci, Yusuf Gagdi, a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben bayan rikici kan sakamakon farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Filato - APC ta sauya sakamakon zaben fitar da gwani na kujerar majalisar wakilan mazabar Pankshin/Kanke/Kanam da ke jihar Plateau, inda ta ayyana Yusuf Adamu Gagdi a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben.

An sanar da sauyin ne ranar Litinin a sakatariyar APC ta jihar Plateau da ke Jos ta bakin shugabar kwamitin gudanar da zabukan fitar da gwani na jam’iyyar, Stella Okotete.

Kara karanta wannan

APC ta hana 'yan siyasa 47 shiga takarar sanata, ta saki cikakken jerin sunayen

APC ta mayar da tikitin takarar mazabar Pankshin/Kanke/Kanam ga Yusuf Gagdi.
Yusuf Gagdi, dan majalisar mazabar Pankshin/Kanke/Kanam da APC ta ba tikiti a Filato. Hoto: @YusufAdamuGagdi
Source: Facebook

APC ta sauya sakamakon zabe a Filato

Okotete ta bayyana cewa sakamakon farko da aka sanar wanda ya ayyana Dr. John Tongshinen a matsayin wanda ya yi nasara ba shi da inganci, a cewar rahoton Punch.

Shugabar kwamitin gudanar da zaben ta jaddada cewa wanda ba shi da ikon sanar da sakamakon ne ya fito ya bayyana shi, don haka ba shi da inganci.

Stella Okotete ta yi nuni da cewa wanda kawai ke da ikon sanar da sakamakon zaben fitar da gwani shi ne jami’in tattara sakamako da aka nada a hukumance, Nandom Kura.

Ta ce:

“Duk wani sakamako da aka sanar ba tare da bin wannan ka’ida ba ba shi da inganci kuma ya kamata jama’a su yi watsi da shi.”

Bayan wannan bayani ne Nandom Kura ya bayyana Yusuf Gagdi a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na APC na mazabar PKK da aka gudanar ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa da wasu wakilai 2 sun sha 'kasa a zaben tsiada gwanin APC a Nasarawa

Yadda aka sanar da sakamakon farko

Tun da farko dai wani jami’i mai suna Monday Daspan ya sanar da Dr. John Tongshinen a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani a hedikwatar mazabar da ke Pankshin ranar Lahadi.

Daspan ya ce Tongshinen ya samu kuri’u 29,968 yayin da Yusuf Gagdi ya samu kuri’u 5,849. A sanarwar farko, Daspan ya bayyana cewa:

“Da ikon da aka ba ni a matsayin shugaban wannan kwamiti, ina ayyana Dr. John Tongshinen a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na mazabar Pankshin/Kanke/Kanam.”
Layla Ali Othman ta taya mijinta Yusuf Gagdi murnar samun tikitin takara a APC.
Laila Ali Othman tare da mijinta Yusuf Adamu Gagdi. Hoto: Yusuf Adamu Gagdi PhD., OON
Source: Facebook

Layla ta taya mijinta Gagdi murna

Laylah Ali Othman, mai dakin Yusuf Gagdi, ta saki bidiyon lokacin da ake ayyana nasarar mijinta a shafinta na Facebook, kuma ta taya shi murna.

"Ina taya mijina, Rt. Hon. Yusuf Adamu Gagdi murnar nasarar da ya samu a zaben fitar da gwani na mazabar PKK a Jos. Kokarinka, salon shugabancinka da jajurcewarka ga al'ummar Pankshin, Kanke, da Kanam za su ci gaba da zama abin koyi ga mutane.

Kara karanta wannan

APC: Akpabio, Barau Jibrin da gwamnoni 7 za su fafata a neman takarar sanata yau

"Ina rokon Allah ya sanya wannan nasarar ta zamo mafarin babbar nasara a gare ka, kuma nasarar da za ta shafi rayuwar al'umma. Ina taya ga murna sahibi na. Ga Allah muka dogara."

- Laylah Ali Othman.

Kalli bidiyon a kasa:

Wanene Yusuf Adamu Gagdi?

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, Yusuf Adamu Gagdi shi ne wakilin Pankshin/Kanam/Kanke a majalisar wakilai ta Najeriya a birnin tarayya Abuja.

An haifi Yusuf Adamu Gagdi ne ranar, 5 ga watan Nuwamban 1985 a ƙauyen Gum-Gadgi da ke gundumar Gagdi a ƙaramar hukunar Kanam ta jihar Plateau.

Yusuf Adamu Gagdi ya wakilci mazaɓar Kantana a majalisar dokokin Plateau, inda ya riƙe muƙamin mataimakin kakakin majalisar jihar, kafin ya samu zuwa majalisar wakilai a 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com