Abu Ya Girma: An Tura Sako ga Amurka da Birtaniya don Su Hukunta Sanatan Najeriya
- Lauya mai kare hakkin dan adam, Deji Adeyanju ya bukaci Amurka, Birtaniya da Canada su kakaba wa Sanata Francis Fadaunsi takunkumi
- Ya ce ya shigar da kara ga kasashen uku kan zargin barazanar da aka yi wa mambobin jam'iyyar Accord gabanin zaben Osun
- Ya bukaci ’yan takarar gwamna a Osun su yi Allah-wadai da duk wata barazana ko kira ga tashin hankali da zaben gwamna da ke tafe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun, Nigeriya - Lauyan kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju, ya bukaci gwamnatin Amurka, Birtaniya da Canada su dauki matakin ladabtarwa kan Sanata Francis Fadaunsi.
Lauyan ya tura sakon wannan bukata ga kasashen uku ne bisa zargin sanatan da yin barazana ga mambobin jam’iyyar Accord gabanin zaben gwamnan jihar Osun.

Source: Twitter
Adeyanju ya yi wannan bayani ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na Arise TV, inda yake magana kan yanayin siyasar Osun gabanin zaben gwamna mai zuwa.
Ya bayyana cewa ya shigar da kara ga kasashen uku, yana neman su yi la’akari da kakaba takunkumin biza da sauran matakan ladabtarwa kan sanatan.
Ya kuma bukaci dukkanin manyan ’yan takarar zaben da za a gudanar a Osun su yi Allah-wadai da duk wata barazana, kira ga tashin hankali ko kai hari ga abokan hamayyarsu.
Adeyanju ya soki kalaman Fadaunsi
Lauyan ya ce zargin kalaman Fadaunsi na da matukar tayar da hankali, musamman saboda yadda ya yi ikirarin cewa a kashe mambobin Accord Party.
Ya ce:
“Wannan ya ja hankali na kan kalaman da muka ji yanzu daga Sanata Fadaunsi, wanda abin takaici ya yi barazanar cewa a kashe mambobin Accord Party.”
Adeyanju ya kara da cewa a ganinsa, kalaman na nuna kokarin tunzura mutane su kai hari ga mambobin jam’iyyar.
Ya nemi matakin kasashen waje
Adeyanju ya ce ya kai batun gaban hukumomin Amurka, Birtaniya da Canada ne saboda wadannan kasashe sun dade suna nuna damuwa kan batun dimokuraɗiyya da tashin hankalin siyasa a Najeriya.
A cewarsa, Amurka musamman ta sha nuna sha’awar ganin an gudanar da zabuka cikin lumana tare da mutunta tsarin dimokuraɗiyya.

Source: Twitter
Ya ce manufar karar ita ce jawo hankalin kasashen uku kan zargin barazanar tare da neman su dauki matakin da ya dace, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Ya kuma bukaci hukumomin da ke da alhakin tsaron zabe da gudanar da shi su tabbatar da kare rayukan masu kada kuri’a tare da hana duk wani yunkuri na lalata tsarin dimokuraɗiyya.
Yan sanda sun gayyaci Sanata Fadahunsi
A wani labarin, kun ji cewa ’yan sandan Osun sun gayyaci Sanata Francis Fadahunsi, mai wakiltar mazabar Osun ta Gabas, domin ya yi bayani kan kalamansa da suka yadu a kafafen sada zumunta.
Gayyatar ta biyo bayan ce-ce-ku-cen da ya barke a kafafen sada zumunta kan kalaman sanatan , inda ya umurci magoya bayan APC da su “kashe” ’yan jam’iyyar Accord
Asali: Legit.ng

