Tsohon Shugaban Kasa a Najeriya Ya Mutu Yana cikin Saduwa da Wata Mata? Gaskiya Ta Fito

Tsohon Shugaban Kasa a Najeriya Ya Mutu Yana cikin Saduwa da Wata Mata? Gaskiya Ta Fito

  • Tsohon Ministan Man Fetur, Dan Etete, ya karyata ikirarin cewa shugaban kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha ya rasu a kan wata mata
  • Ya bukaci tsohon jami’in SSS, Dennis Amachree, ya gabatar da rahoton gwajin gawa da sauran takardun da za su tabbatar da ikirarinsa
  • Etete ya ce labarin da Amachree ya bayar bayan shekaru 28 ba komai ba ne face zargi da ba a tabbatar da shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon Ministan Albarkatun Man Fetur, Dan Etete, ya kalubalanci ikirarin cewa tsohon Shugaban Najeriya a mulkin soja, Janar Sani Abacha, ya mutu yayin da yake saduwa da wata mata.

Etete, wanda ya yi aiki a gwamnatin Abacha, ya mayar da martani ne ga ikirarin tsohon jami’in Hukumar Tsaron Farin Kaya (SSS), Dennis Amachree, kan abin da ya faru a sa’o’in karshe na rayuwar Abacha.

Kara karanta wannan

NDC: "Yanzu muka gano dalilin Gwamna Abba na Komawa APC"

Abacha.
Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja, Janar Sani Abacha Hoto: Dan Etete
Source: Twitter

Premium Times ta ce Amachree ya bayyana wannan labari ne a cikin littafinsa mai suna DSS @40: My Journey Behind the Shield, wanda aka wallafa wasu sassan cikinsa a watan Yulin 2026.

A cikin littafinsa, Amachree ya ce Abacha ya mutu da misalin karfe 4:05 na safiyar 8 ga Yuni, 1998 a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja lokacin da yake kwance da wata mata.

Dan Etete ya nemi a kawo hujjoji

A cikin wata sanarwa mai taken “bayan shekaru 28, ba ka da hujja”, Etete ya ce Amachree bai gabatar da wata takarda ko hujja da za ta tabbatar da labarin da ya bayar ba.

Ya tambayi sunan matar da ake zargin tana tare da Abacha, kasarta da kuma ko ta taba tabbatar da labarin da ake danganta mata.

Etete ya kuma bukaci a bayyana inda rahoton gwajin gawar Abacha yake da kuma ko akwai wasu bayanan likitoci da suka tabbatar da dalilin mutuwarsa.

Kara karanta wannan

Bincike ya zo ƙarshe, an ji dalilin Kanal Mohammed Ma'aji na shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Ya ce

“Ya gaya mana lokacin da abin ya faru, ya gaya mana dakin da abin ya faru da kuma abin da aka fada. Shekaru 28 kenan, daga abin da ya tuna, ba tare da wata takarda da ke bayanin hakan ba.”

A cewar Etete, ba a taba gabatar da wannan labari ba a cikin shekaru da suka biyo bayan mutuwar Abacha, duk da cewa an gudanar da bincike da tattaunawa daban-daban kan yadda tsohon shugaban kasar ya mutu.

Ya tambayi dalilin kyale matar

Etete ya kuma tambayi dalilin da ya sa aka bar matar da ake cewa tana tare da Abacha ta bar Najeriya idan har tana da muhimmiyar alaka da binciken mutuwar tsohon shugaban kasar.

Ya nemi a bayyana wanda ya ba da umarnin a sake ta, wanda ya amince da tafiyarta da kuma ko akwai bayanan binciken da suka shafi lamarin.

Dan Etete.
Tsohon ministan albarkatun man fetur a Najeriya, Cif Dan Etete Hoto: @Etetedan
Source: Twitter

Ya ce ba ya magana a matsayin lauyan Abacha ko kakakinsa, sai dai a matsayin wanda ya yi aiki a gwamnatinsa kuma ya san shi da kansa, kamar yadda Punch ta kawo.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta sake girgiza Najeriya, tsohon antoni janar ya riga mu gidan gaskiya

Etete ya kara da cewa mutuwar mutum, musamman tsohon shugaban Najeriya, ba abu ba ne da ya kamata a mayar da shi nishadi ko labarin neman daukar hankali.

Abin da ya yi ajalin Janar Sani Abacha

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin darakta na hukumar tsaron farin kaya (DSS), Dennis Amachree, ya yi magana kan mutuwar marigayi Janar Sani Abacha.

Dennis Amachree ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar na mulkin soja, ya rasu ne sakamakon bugun zuciya.

Amachree ya bayyana cewa babbar ganau ba jiyau ba kan lamarin wata mace ce da take tare da Abacha jim kaɗan kafin mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262