APC Ta Fitar da Jerin Sunayen 'Yan Takararta na Sanatoci a 2027? Jam'iyyar Ta Yi Bayani

APC Ta Fitar da Jerin Sunayen 'Yan Takararta na Sanatoci a 2027? Jam'iyyar Ta Yi Bayani

  • Jam'iyyar APC ta yi martani ka. rahoton da ke yawo cewa ta fitar da cikakken jerin sunayen 'yan takararta na majalisar dattawa na zaben shekarar 2027
  • Felix Morka, mai magana da yawun jam'iyyar APC, ya fitar da sanarwa inda ya yi bayani kan jerin sunayen da ke yawo
  • Kakakin na APC ya ce jerin sunayen na ƙarya ne na gaba ɗaya, kuma ya buƙaci mambobin jam'iyyar, kafafen yaɗa labarai da su yi watsi da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta yi magana kan jerin sunayen da ke yawo na 'yan takararta na kujerun majalisar dattawa a zaben 2027.

APC ta jaddada cewa jerin sunayen da ke yawo a dandalin sada zumunta da wasu kafafen intanet na ƙarya ne gaba ɗaya kuma ba su fito daga jam'iyyar ba.

Kara karanta wannan

PDP ta kara birkicewa, 'yan majalisa 4 na jam'iyyar daga Bauchi sun koma APM

APC ta musanta fitar da sunayen 'yan takarar sanata
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Facebook

APC ta yi magana kan sunayen 'yan takara

Felix Morka, sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam'iyyar, ya musanta jerin sunayen da ke yawo a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, 4 ga Yuni, 2027 a shafin X.

Kakakin na APC ya yi kira ga mambobin jam'iyyar, kafafen yaɗa labarai, da sauran jama'a da su yi watsi da jerin sunayen da ke yawon.

Ya kuma yi kira ga mambobin jam'iyyar da masu ruwa da tsaki da su daina yada jerin sunayen domin suna haifar da ruɗani da yaudarar jama'a.

APC ta karyata sunayen da ke yawo

Wani ɓangare na sanarwar yana cewa:

"Hankalin jam'iyyar APC ya karkata ga wani "Jerin sunayen da aka kammala na 'yan takarar sanatan APC zuwa yanzu" wanda ke yawo a halin yanzu a dandalin sada zumunta da wasu kafafen intanet."
"APC tana son bayyana cewa gabadaya jerin sunayen na karya ne, kuma bai fito daga jam'iyyar ba."

Kara karanta wannan

Bayan sace yayar tsohon minista, ƴan bindiga sun harbe shugaban jam'iyyar adawa

"Jam'iyyar tana sake jaddada cewa kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na APC ne kawai, ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwarsa da aka amince da su bisa doka, ke da ikon sanar da jerin sunayen 'yan takarar da suka yi nasara a zaɓubbukan fitar da gwani da sauran tsare-tsare da tsarin mulki ya tanada."
"Muna buƙatar dukkan mambobin jam'iyyar da masu ruwa da tsaki da su guji yaɗa bayanan da ba a tantance ba waɗanda ke da ikon haifar da ruɗani, yaudarar jama'a ko gurgunta mutuncin hanyoyin dimokuraɗiyya na jam'iyyar."
APC ta karyata fitar da sunayen 'yan takarar sanata
Farfesa Nentawe Yilwatda, shugaban APC na kasa Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

'Yan majalisa sun fice daga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mambobi uku na majalisar wakilai sun mika takardar ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

'Yan Majalisar wakilan sun sanar da sauya shekarsu daga APC zuwa jam'iyyun adawa na PRP da ADC a hukumance a ranar Laraba, 3 ga watan Yunin 2026.

Daga cikin 'yan majalisar da suka bar APC akwai Hon. Rabilu Bala, mai wakiltar mazabar Jama'are/Itas-Gadau ta jihar Bauchi, wanda ya koma jam'iyyar PRP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng