Zaben Fitar da Gwani: Manyan 'Yan Majalisa na APC da Suka Gaza Samun Tikitin Komawa

Zaben Fitar da Gwani: Manyan 'Yan Majalisa na APC da Suka Gaza Samun Tikitin Komawa

FCT, Abuja - Wasu 'yan Majalisar wakilai masu ci a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC sun rasa damar samun tikitin takarar sake zaɓensu yayin zaɓubbukan fitar da gwani.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jam'iyyar APC dai ta gudanar da mafi yawan zabubbukan fitar da gwani na kujerun 'yan majalisar wakilai a ranar Asabar, 16 ga watan Mayun 2026.

Yusuf Gagdi na cikin 'yan majalisar wakilai da suka rasa tikitin APC
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Julius Ihonvbere, Yusuf Gagdi da Yusuf Saidu Miga Hoto: Julius Ihonvbere, Rt Hon Yusuf Gagdi, Anas Abdulrahman
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro manyan 'yan majalisar wakilai da suka gaza samun tikitin APC domin sake komawa kan kujerunsu.

An sanar da sakamakon zaɓen fitar da gwanin na jam'iyyar APC a mazaɓu da dama a faɗin jihohi ranar Lahadi, 17 ga watan Mayun 2026.

Yayin da 'yan majalisar wakilai da masu neman takara da dama suka samu tikiti, sakamakon da aka fitar ya nuna cewa wasu mambobi masu ci sun sha kaye a hannun sauran masu neman takarar.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa da wasu wakilai 2 sun sha 'kasa a zaben tsiada gwanin APC a Nasarawa

1. Julius Ihonvbere

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Julius Ihonvbere, ya rasa zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC na mazaɓar tarayya ta Owan ta Yamma da Owan ta Gabas a jihar Edo.

Kelvin Muhammed, jami’an da ya jagoranci zaɓen, shi ne ya sanar da sakamakon zaɓen fitar da gwanin a ofishin jam’iyyar na Afuze.

Yayin da yake sanar da sakamakon a cikin wani bidiyo da NTA Uzairue ta wallafa a Youtube, Kelvin Muhammed ya ce masu neman takara guda biyar ne suka fafata a zaɓen fitar da gwanin.

Julius Ihonvbere ya rasa tikitin APC
Julius Ihonvbere na jawabi a zauren majalisar wakilai Hoto: Julius Ihonvbere
Source: Facebook

Jami’in da ya jagoranci zaɓen ya ce Andrew Ijegbia, tsohon kwamishinan ma’adinai na jihar Edo, ya lashe zaɓen bayan da ya samu ƙuri’u 3,695.

Wannan sakamako yana nufin cewa Ihonvbere ya rasa damarsa na komawa kan kujerar a wa’adi na uku.

Sai dai, Julius Ihonvbere, ya yi ikirarin samun nasara a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC na mazaɓar Owan ta Gabas/Owan ta Yamma a jihar Edo, jaridar The Guardian ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

'Yan majalisar wakilai na APC da suka sha kaye a zaben fitar da gwani

Bangaren ɗan majalisar ya bayyana cewa sakamakon da aka tattara daga mazaɓu na zaɓen kato bayan kato da aka gudanar a faɗin mazaɓar ya nuna cewa Ihonvbere ya samu ƙuri’u 4,729.

Sun ce ya doke babban abokin hamayyarsa, Hon. Andrew Ijegbai, wanda ya samu ƙuri’u 2,912, yayin da Hon. Abdul Oroh ya sami ƙuri’u 29.

2. Yusuf Gagdi

A jihar Plateau kuwa, Yusuf Gagdi, mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Pankshin/Kanke/Kanam kuma shugaban kwamitin Majalisar kan rundunar sojojin ruwa, ya gaza samun tikitin takarar wa’adi na uku.

Yusuf Gagdi ya rasa tikitin APC
Yusuf Gagdi a zauren majalisar wakilan Najeriya Hoto: Rt Hon Yusuf Gagdi
Source: Facebook

Yusuf Gagdi ya samu ƙuri’u 5,849 inda ya sha kaye a hannun Dr. John Tongshinen, wanda ya tattara ƙuri’u 29,968 a zaɓen fitar da gwanin na kato bayan kato, tashar TVC News ta kawo labarin.

An bayyana sakamakon ne a hedikwatar mazaɓar da ke Pankshin ranar Lahadi, 17 ga watan Mayun 2026.

3. Mansur Musa Jega

A jihar Kebbi, ɗan majalisa mai ci Mansur Musa Jega ya rasa tikitin APC na Mazaɓar Tarayya ta Jega/Gwandu/Aleiro, cewar rahoton TheCable.

Mansur Musa Jega ya rasa tikitin APC
Dan majalisar wakilan Najeriya, Mansur Musa Jega Hoto: Mansur Musa Jega
Source: Facebook

Mansur Musa ya rasa tikitin ne sakamakon wani tsari na maslaha wanda ya samar da tsohon shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya, Jafar Ahmed Jega.

Kara karanta wannan

Yusuf Buhari ya san matsayarsa bayan kammala zaben fitar da gwani na APC a Katsina

4. Yusuf Saidu Miga

Dan majalisar wakilai mai wakiltar Jahun/Miga a jihar Jigawa, Yusuf Saidu Miga, bai kai labari ba a zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC, jaridar The Punch ta kawo labarin

Yusuf Saidu Miga ya rasa tikitin APC
Dan majalisar wakilai mai wakiltar Jahun/Miga, Yusuf Saidu Miga Hoto: Anas Abdulrahman
Source: Facebook

Yusuf Saidu Miga wanda ake yi wa kallon ɗaya daga cikin ’yan majalisa mafi daɗewa a kan kujera daga Jigawa, ya fara shiga Majalisar Wakilai ne a shekarar 2003 a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ANPP.

Daga baya ya koma jam’iyyar APC lokacin haɗakar jam’iyyun hamayya a shekarar 2014 wadda ta kai jam’iyyar ga mulki a shekarar 2015.

5. Nicholas Mutu

Zaɓen fitar da gwanin ya kuma haifar da gagarumin babban mamaki a jihar Delta, inda ɗan majalisar tarayya na dogon lokaci, Nicholas Mutu, ya gaza samun tikitin APC na mazaɓar tarayya ta Bomadi/Patani, rahoton Vanguard ya tabbatar da hakan.

Nicholas Mutu ya rasa tikitin APC
Dan majalisar wakilai, Nicholas Mutu Hoto: Nicholas Mutu
Source: Facebook

Nicholas Mutu, wanda ya wakilci mazaɓar a Majalisar wakilai tun shekarar 1999, ya rasa tikitin jam’iyyar ne a hannun Basil Okolobaowei Ganagana, wanda ya fito a matsayin mai riƙe da tutar APC gabannin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Jerin masu neman takarar majalisar tarayya da APC ta yi watsi da su a wurin tantancewa

Sanata Maidoki ya fice daga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta gamu da cikas bayan ficewar daya daga cikin sanatocinta a jihar Kebbi.

Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu a Majalisar dattawa, Garba Musa Maidoki, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC.

Maidoki ya ɗora alhakin shawararsa a kan dambarwar cikin gida da ta daɗe tana faruwa a cikin jam’iyyar, ya bayyana cewa lamarin ya yi tasiri mara kyau ga burinsa na siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng