Majalisar Wakilai: Yusuf Buhari da Fitattun Ƴan Arewa 7 da Suka Samu Tikitin APC

Majalisar Wakilai: Yusuf Buhari da Fitattun Ƴan Arewa 7 da Suka Samu Tikitin APC

Jam’iyyar APC ta gudanar da zabukan fidda gwani na kujerun majalisar wakilai a sassa daban-daban na Najeriya, inda aka samu manyan sauye-sauye a siyasa gabanin babban zaben 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Zabukan, wadanda su ne farkon jerin zabukan fitar da gwani na jam’iyyar mai mulki, sun bai wa wasu fitattun ‘yan siyasa damar ƙara karfafa matsayinsu, yayin da wasu kuma suka fuskanci babban koma baya duk da tasirinsu a siyasa.

An samu wasu fitattun mutane da suka lashe zaben fitar da gwnai na jam'iyyar APC a majalisar wakilai daga Arewa.
Hagu zuwa dama: Rafiu Ajakaye (Kwara) da Yusuf Buhari (Katsina) da Abbas Tajudeen (Kaduna). Hoto: Isaac Alabi, Yusuf Buhari, Abbas Tajudeen
Source: Facebook

A wasu jihohi, tsofaffin ‘yan majalisa sun samu damar sake komawa takara karo na uku ko fiye da haka, yayin da sababbin ‘yan takara suka samu damar shiga sahun gaba a siyasar APC, in ji rahoton Daily Trust.

APC: Manyan wadanda suka lashe zabe a Arewa

Ga jerin manyan masu neman takara da suka lashe zaben fitar da gwani na majalisar wakilai a APC:

Kara karanta wannan

Rigima ta barke bayan zaben fitar da gwanin APC, an kashe mutum 1 a jihar Kaduna

1. Abbas Tajudeen

Tajudeen Abbas ya lashe tikitin majalisar wakilai a APC
Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas yana jagorantar zaman majalisa a Abuja. Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

Daya daga cikin manyan wadanda suka yi nasara shi ne Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, wanda ya samu tikitin APC domin sake neman kujerarsa karo na biyar a jihar Kaduna.

Nasararsa ta kara nuna irin karfin da yake da shi a cikin APC da kuma matsayin shugabancinsa a majalisar wakilai, a cewar rahoton The Nation.

Rahotanni sun nuna cewa fitowarsa ba tare da wata babbar adawa ba ya kara tabbatar da tasirinsa a cikin jam’iyyar.

2. Yusuf Buhari

Yusuf Buhari ya lashe tikitin takarar majalisar wakilai don wakiltar Daura/Sandamu/Mai’adua
Yusuf Buhari, 'da ga marigayi Shugaba Muhammadu Buhari da ya lashe tikitin APC a Daura/Sandamu/Mai’adua. Hoto: Yusuf Buhari
Source: Facebook

Wani daga cikin fitattun wadanda suka yi nasara shi ne Yusuf Buhari, ɗan marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Legit Hausa ta ruwaito cewa, Yusuf Buhari ya samu tikitin APC don wakiltar mazabar Daura/Sandamu/Mai’adua a jihar Katsina, lamarin da ya sanya shi shiga harkar siyasa karo na farko.

Masu sharhi na ganin shigarsa siyasa wata alama ce ta ci gaba da tasirin siyasar iyalan Buhari a APC da Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Ribas: Mutumin Wike na dab da zama 'dan takarar gwamnan APC bayan Fubara ya janye

3. Yusuf Gagdi

Yusuf Adamu Gagdi ya lashe tikitin takarar majalisar wakilai karo na uku a APC
Yusuf Gagdi, dan majalisar mazabar Pankshin/Kanke/Kanam da APC ta ba tikiti a Filato. Hoto: Yusuf Adamu Gagdi
Source: Facebook

A jihar Plateau, dan majalisa Yusuf Adamu Gagdi ya sake samun tikitin APC bayan jam’iyyar ta soke sakamakon farko da ya bayyana John Tongshinen a matsayin wanda ya yi nasara.

Shugabar kwamitin zaben fidda gwani na APC a Plateau, Stella Okotete, ta bayyana cewa sanarwar farko ba bisa ka’ida aka yi ta ba, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Daga bisani, APC ta tabbatar da Yusuf Gagdi a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben fidda gwani na mazabar Pankshin/Kanke/Kanam.

4. Adamu Abubakar

Adamu Abubakar, 'da ga tsohon shugaban mulkin soja Janar Abdulsalami Abubakar, ya samu nasara a zaben fitar da gwani na mazabar Chanchaga da ke jihar Neja.

Nasararsa ta kara dawo da sunan iyalan Abdulsalami cikin siyasar zamani, musamman a APC, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

5. Kaumi Zulum

Kaumi Umara Zulum ya lashe tikitin majalisar wakilai na APC a mazabar Dikwa/Konduga/Mafa
Kaumi Umara Zulum, dan uwa ga Gwamna Babagana Zulum ya na daga hannu a wani gangamin siyasa. Hoto: Hon Mohammed Sheriff
Source: Facebook

A jihar Borno, Dr. Kaumi Umara Zulum, wanda kani ne ga gwamna Babagana Umara Zulum, ya samu tikitin APC ba tare da hamayya ba.

Kara karanta wannan

APC ta hana 'yan siyasa 47 shiga takarar sanata, ta saki cikakken jerin sunayen

Kaumi Zulum zai nemi maye gurbin Hon. Ibrahim Mohammed Buja a mazabar Dikwa/Konduga/Mafa, in ji rahoton Business Day.

Ko da yake ba shi da gogewar aiki a majalisa, nasararsa ta nuna irin goyon bayan da yake samu daga manyan masu ruwa da tsaki a jihar.

6. Abdulquawiy Olododo

Abdulquawiy Olododo ya samu tikitin takarar APC a jihar Kwara
Abdulquawiy Olododo, kwamishina a KWara da ya samu tikitin takarar majalisar wakilai a APC. Hoto: @followKWSG
Source: Twitter

A jihar Kwara, Abdulquawiy Olododo ya samu nasara bayan ya doke dan majalisa mai ci, Yinka Aluko, wanda aka fi sani da “Original Home Boy” a cewar rahoton Punch.

Olododo, wanda kwamishina ne a gwamnatin jihar, ya samu goyon baya daga manyan jiga-jigan APC kafin zaben. Idan ya yi nasara a babban zabe, zai wakilci mazabar Ilorin ta Gabas/Ilorin ta Kudu a majalisar wakilai.

7. Leke Abejide

Leke Abejide ya lashe tikitin takara a APC
Dan majalisa, Leke Abejide ya lashe tikitin takara a jam'iyyar APC. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

A jihar Kogi, jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Leke Abejide ya samu tikitin APC bayan sauya sheka daga jam’iyyar ADC.

Tun da farko, wasu sun yi zargin cewa karfinsa na siyasa yana da nasaba ne da ADC kawai, amma sakamakon zaben APC ya nuna yana da farin jini a mazabarsa.

Nasararsa ta nuna cewa wasu ‘yan siyasa na iya ci gaba da samun goyon bayan jama’a ko da bayan sun sauya jam’iyya.

Kara karanta wannan

'Ya'yan tsofaffin shugaban kasa da gwamnoni da suka samu takarar majalisar wakilai a APC

8. Rafiu Ajakaye

Rafiu Ajakaye ya lashe tikitin APC a mazabar Offa/Oyun/Ifelodun, jihar Kwara.
Rafiu Ajakaye, tsohon mai magana da yawun gwamnan Kwara da ya zama dan takarar APC. Hoto: Isaac Alabi
Source: Facebook

Har ila yau, tsohon mai magana da yawun gwamnan Kwara, Rafiu Ajakaye, ya zama daya daga cikin fitattun wadanda suka yi nasara a zabukan, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya kayar da dan majalisa mai ci, Ismail Tijani, wanda ke wakiltar Offa/Oyun/Ifelodun. Masu sharhi na ganin nasararsa wata alama ce ta sabon sauyin karfi a siyasar APC ta jihar Kwara.

'Yan majalisar wakilai da suka sha kasa a APC

A wani labari, mun ruwaito cewa, APC mai mulki a Najeriya ta gudanar da zaben fitar da gwani domin zabar 'yan takarar da za su nemi kujerun majalisar wakilai a zaben 2027.

Wasu daga cikin 'yan majalisar da ke kan kujera sun shiga cikin zaben domin neman damar sake wakiltar mazabunsu, kuma sun yi nasara, kamar kakakin majalisa, Abbas Tajudeen.

Sai dai, daga cikin 'yan majalisun da ke kan kujera, wasu sun gaza samun tikitin sake tsayawa takara a zaben 2027, kamar Matthew Nwogu mai wakiltar Aboh Mbaise/Ngor Okpala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com