Trump Ya Sake Cika Baki kan Mashigar Hormuz da Ake Takaddama a Kai

Trump Ya Sake Cika Baki kan Mashigar Hormuz da Ake Takaddama a Kai

  • Donald Trump da ke matsayin shugaban kasar Amurka, ya bayyana kasar da ke da cikakken iko kan mashigar Hormuz
  • Shugana Donald Trump ya ce ba ya yarda da Iran, yana zargin kasar da yi masa ƙarya da karairayi akai-akai
  • Mohsen Rezaei ya ce ba za a sake buɗe mashigar Hormuz ba har sai Amurka ta sauya halayenta kuma ta amince da sharuɗɗan Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce halin da ake ciki da Iran yana tafiya yadda ya kamata.

Shugaba Donald Trump ya kuma bayyana cewa dakarun Amurka sun mallaki cikakken iko kan mashigar Hormuz.

Trump ya ce Amurka na da iko kan Hormuz
Shugaba Donald Trump na Amurka a Oval Ofis Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a Joint Base Andrews.

Me Trump ya ce kan mashigar Hormuz?

Kara karanta wannan

Trump ya ajiye takama, ya mika bukata ga Iran yana so a biya masa ita

“Iran na tafiya lafiya, komai yana tafiya daidai. Muna da cikakken iko kan mashigar Hormuz. Muna iko da ita; babu wani da ke iko da ita sai mu. Rundunar sojin ruwanmu abin mamaki ce, kuma abubuwa suna tafiya yadda ya kamata ga kasarmu,” in ji Trump

Shugaban kasar na Amurka ya ƙara da cewa ba ya amincewa da Iran saboda abin da ya kira karairayin da ta yi masa.

“Ban yarda da Iran ba. Ni ne mutum na ƙarshe da zai yarda da Iran; sun yi mini ƙarya akai-akai. A yanzu muna da cikakken iko kan mashigar Hormuz; su ba su da iko."

- Shugaba Donald Trump

Iran ta yi martani

Mohsen Rezaei, sakataren Majalisar Koli ta Tsaron Ƙasa ta Iran, ya shaida wa jakadan China cewa ba za a buɗe mashigar Hormuz ba har sai Amurka ta sauya halayenta kuma ta amince da sharuɗɗan Iran, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Iran, Tasnim, ya ruwaito

Rezaei ya ce Amurka ce “tushen rashin tsaro” a yankin Gulf, mashigar Hormuz da kuma tekun Oman, yana zargin Washington da ƙaddamar da “yaƙin da bai dace da doka ba” wanda ya jefa yankin gaba ɗaya cikin haɗari.

Ya ce dole Washington ta kawo ƙarshen yaƙin tare da sakin kuɗaɗen Iran da aka rike, baya ga kawo ƙarshen rikice-rikicen da ke faruwa a yankin, ciki har da na Lebanon da Gaza.

Kara karanta wannan

Yadda barazanar Iran ta firgita Trump, ya sauya jirgi saboda tsoron kashe shi

Rezaei ya ƙara da cewa duk wata yarjejeniya tsakanin Iran da Oman kan wata hanya da za ta bi ta mashigar Hormuz zai kasance daban da babban batun rufe mashigar.

Trump ya ce Iran ta kwace mashigar Hormuz
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kamfanin Trump ya tafka asara

A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin yada labarai na shugaban kasar, Amurka Donald Trump, Trump Media & Technology Group (TMTG), ya bayyana asarar da ya tafka mai girma.

Kamfanin na Trump ya bayyana cewa ya yi asarar dala miliyan $238 a zangon watanni uku na biyu na 2026, duk da samun kudin shiga na $1.7m.

TMTG ya ce mafi yawan asarar ta samo ne daga dala miliyan 190.4 da suka shafi asarar da ba a tabbatar da ita ba kan kadarorin dijital.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng