Mariya Abdullahi: Matar da Ta Lashe Zaɓen Majalisar Tarayya a Katsina Shekaru 35 da Suka Wuce
Katsina, Nigeria - A makonnin da suka gabata ne jam'iyyar APC ta tsaida Hajiya Jamila Abdu Mani a matsayin yan takarar kujerar Majalisar wakilai ta mazabar Mani/Bindawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wannan lamari ya haifar da ce-ce-ku-ce a ciki da wajen jihar Katsina, inda wasu le goyon baya, wasu kuma na ganin cewa tsaida mace takara har ta yi shugabanci ya saba wa addinin musulunci.

Source: Facebook
Premium Times ta ruwaito cewa wasu malamai daga kananan hukumomin Mani da Bindawa sun nuna adawarsu da wannan mataki, a cewarsu bai halatta mace ta yi shugabanci ba.
Mace ta taba cin kujerar Majalisar tarayya
Sai dai a binciken da Legit Hausa ta gudanar, mun gano cewa an taba samun mace da ta lashe zaben kujerar Majalisar Wakilan tarayya daga jihar Katsina shekaru 35 da suka gaba.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta kulla sabuwar yarjejeniya da Jamus, za a kashe €65m a Najeriya
Hajiya Mariya Abdullahi ta samu nasarar zama yar Majalisa mai wakiltar mazabar Bakori da Danja a Majalisar tarayya a zaben 1991.
Tsohuwar yar Majalisar ta bayyana kalubalen da ta fuskanta lokacin zabe, ciki har da batun kasancewarta mace kuma musulma, amma ta ce duk da haka ta yi nasara.
Gwamnatin sojan Ibrahim Babangida ta gudanar da zaben majalisa, sai dai Janar Sani Abacha ya rantsar da su bayan 'yan watanni a ofis.
Abubuwan sani game da Mariya Abdullahi
A wannan rahoton, mun tattaro muku abubuwan da ya kamata ku sani game da mace ta farko da ta taba zama yar Majalisar tarayya daga jihar Katsina.
1. Takaitaccen tarihin Hajiya Mariya
An haifi Hajiya Marigayi Abdullahi a garin Bakori da ke yankin Funtua a jihar Katsina fiye da shekaru 60 da suka gabata, kamar yadda ta bayyana a wata hita da kafar watsa labarai ta Manhaja Blueprint.
Matar ta yi karatun firamare a makarantar kwana ta St.Barths Boarding da ke Wusasa, kafin daga bisani ta shiga makarantar sakandire ta mata 'Queens College' da ke Kaduna.
Mariya ta bayyana cewa ta bar wannan makaranta kafin su yi jarabawar karshe bisa wasu dalilai, inda ta karisa karatun sakandire a makarantar Saints Maria Goretti da ke Benin a 1971.

Source: Facebook
Daga nan ta tafi kasar Ingila ta yi karatun Diploma a Makarantar ‘London School of television production. Sannan ta dawo ta yi karatun digiri a jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa, Bauchi a kan ‘Business Management’ watau tattalin kasuwanci.
2. Ayyukan da ta yi kafin shiga siyasa
Hajiya Mariya ta kasance yar jarida kuma ta yi aiki a kafafen watsa labarai da dama na tsawon shekaru 16 kafin ta shiga harkokin siyasa.
Daga cikin ayyukan da ta yi akwai na gidan Radiyo Nigeria Kaduna a matsayin mai gabatarwa, kuma ta jagoranci gudanar da shirye-shirye da dama kamar ‘don iyalanku’ da shirye shiryen kiyon lafiya da sauran su.
3. Shugabancin Bakori
Bayan shafe tsawon ahekaru tana aikin jarida, Hajiya Mariya ta nemi taiarar kujerar shugaban karamar hukumar Bakori kuma ta samu nasara a 1990.
"Kujerar da na fara yin takara ita ce kujerar shugabar ƙaramar hukumar Bakori a shekarar 1990 a inuwar jam’iyar SDP kuma Allah ya ba ni nasara na ci zaɓe," in ji ta.
A wata hira da DW Hausa, Mariya Abdullahi ta ce ta fuskanci kalubale a wannan lokaci saboda karfin da aka ba kansiloli, wanda ya ba su damar tsige ciyaman a kan kuskure karami.
4. Zuwa majalisar wakilai a 1991
Hajiya Mariya Abdullahi ya lashe zaben Majalisar wakilai mai wakiltar Bakori/Danja a zaben 1992, kuma bayan watanni shida aka rantsar da su a shekarar 1992.
Tsohuwar yan Majalisar ta ce ta shafe kusan shekara guda a majalisa kafin tsohon shugaban kasa, Sani Abacha ya karbi mulki, inda ya rushe dukkan jam'iyyu a 1993, wanda hakan ya sa ta koma gida.

Source: Twitter
5. Mukamin kwamishina
Bayan dawowa gida, an nada Mariya Abdullahi a muƙamin babbar darakta a ma’aikatar Kasuwanci da masana’antu a 1994, daga bisani aka maida ita kujerar babbar sakatariya a ma'aikatar mata.
A shekarar 1999, da aka koma mulkin demokuradiyya, gwamnan Katsina na farko, Marigayi Umaru Musa Yar'adua ya nada ta a matsayin kwamishinar yada labarai da al'adu.
Daga bisani, Umaru Musa ya maida Hajiya Mariya ma’aikatar jin daɗi da walwala, raya karkara da kuma kula da ci gaban matasa lokacin da ya yi garambawul a majalisar kwamishinoni.
Malamai sun soki takarar mace a Katsina
A wani labarin, kun ji cewa malaman addinin musulunci sun yi fatali da matakin tsaida mace a matsayin 'yar takarar kujerar Majalisar wakilai a mazabar Mani da Bindawa.
Malaman guda biyu sun bukaci al’umma da kada su zabi +amila Abdu-Mani, ‘yar takarar APC a zaben majalisar wakilai na 2027, suna mai cewa zaben kace ya saba wa shari'a.
Sai dai wannan matsaya ta malaman ta saba wa fahimtat babban kwamandan rundunar Hisbah na jihar Katsina, Sheikh Abu Ammar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


