'Yan Majalisun da Suka Fice daga APC bayan Rasa Tikitin Takara a 2027
FCT, Abuja - Wasu 'yan majalisu sun rasa tikitin tsayawa takara na jam'iyyar APC domin fafatawa a babban zaben shekarar 2027.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Wasu daga cikin 'yan majalisun da suka rasa tikitin takarar, sun dauki matakin ficewa daga jam'iyyar mai mulki.

Source: Facebook
'Yan majalisu sun bar APC saboda rasa takara
Legit Hausa ta tattaro 'yan majalisun da APC ta hana tikitin takara a 2027, wadanda suka fice daga jam'iyyar domin gwada sa'arsu a wasu jam'iyyun.
Daga cikin wadanda suka fice daga APC akwai mai rike da kujerar sanata, sauran kuma mambobi ne a Majalisar wakilai.
Ga jerinsu nan kasa:
1. Sanata Anthony Siyako Yaro (Jihar Gombe)
Sanata mai wakiltar Gombe ta Kudu a Majalisar dattawa, Anthony Siyako Yaro, ya raba gari da jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Source: Facebook
Anthony Siyako Yaro ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP bayan ya gaza samun tikitin takarar sanata na jam’iyya mai mulki don zaɓen 2027.
Sanatan ya bayyana hakan ne a cikin sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 9 ga watan Mayun 2026 wadda aka sanya a shafin Facebook.
2. Abdullahi El-Rasheed (Jihar Gombe)
Dan Majalisar wakilai mai wakiltar Dukku/Nafada daga jihar Gombe, Hon. Abdullahi El-Rasheed, wanda aka fi sani da Bala Kelly, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC.
Jaridar Daily Trust ta ce Hon Abdullahi El-Rasheed ya fice daga APC ne bayan ya gaza samun tikitin takarar mazaɓar Dukku/Nafada a ƙarƙashin tsarin maslaha na jam’iyyar.
Ɗan majalisar ya sanar da matakin nasa ne a cikin wata wasiƙa da ya aika wa shugaban APC na mazaɓar Waziri ta Arewa, ƙaramar hukumar Dukku, jihar Gombe.

Source: Facebook
El-Rasheed, wanda aka zaɓa a shekarar 2023 a ƙarƙashin inuwar PDP, ya bar jam’iyyar ne ya koma APC a watan Fabrairun 2026.
Sai dai zaman sa a APC bai daɗe ba bayan da tsarin maslaha na jam’iyyar a Gombe ya samar da Alhaji Jamilu Ahmed Shabewa a matsayin ɗan takarar kujerar Majalisar wakilai ta mazaɓar Dukku/Nafada.
Abdullahi El-Rasheed, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce rashin samun tikitin takarar a ƙarƙashin APC ba shi ne sakamakon da ya yi addu’ar samu ba, inda ya buƙaci magoya bayansa da su kwantar da hankulansu su jira mataki na gaba da zai ɗauka.
3. Shehu Dalhatu Tafoki (Jihar Katsina)
Dan Majalisar wakilai mai wakiltar Kankara/Faskari/Sabuwa daga Jihar Katsina, Shehu Dalhatu Tafoki, ya fice daga jam'iyyar APC.

Source: Facebook
Shehu Dalhatu Tafoki ya sauya sheƙa APC zuwa jam’iyyar PDP bayan ya gaza samun tikitin takara ta hanyar maslaha don babban zaɓen 2027, jaridar Premium Times ta kawo rahoton.
Tuni dan majalisar ya sayi fom ɗin na gani ina so da na tsayawa takara na jam’iyyar PDP bayan sauya sheka zuwa cikinta, ita kuwa APC ta tsaida Hamzah Sukaiman Fasakari
Jam’iyyar APC a jihar Katsina ta yanke shawarar zaɓar ’yan takararta na babban zaɓen 2027 ne ta hanyar tsarin maslaha.
4. Sani Lawal (Jihar Katsina)
Haka kuma, dan majalisa mai wakiltar Zango/Baure daga jihar Katsina, Hon. Sani Lawal, ya raba gari da jam'iyyar APC mai mulki.

Source: Twitter
Hon. Sani Lawal ya fice daga jam'iyyar APC ne bayan tsarin maslaha da aka yi amfani da shi wajen zabar 'yan takara, ya sanya ya rasa tikitin jam'iyyar domin sake neman komawa kan kujerarsa a 2027.
Dan majalisa mai wakiltar Kankia/Kusada/Ingawa, Abubakar Yahaya Kusada, ya sanar da sauya shekar Hon. Sani Lawal a shafinsa na X a ranar Litinin, 11 ga watan Mayun 2026.
Hon. Abubakar Yahaya Kusada ya bayyana cewa dan majalisar bai sanar da jam'iyyar da zai koma ba bayan ficewarsa daga APC.
Jam'iyyar APC ta tara N4.4bn
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta tara makudan kudade ta hanyar sayar da fom ga masu neman tsayawa takara a zaben 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar APC ta tara sama da Naira biliyan 4.45 daga sayar da fom ɗin nuna sha’awar tsaya wa takara.
APC ta samu Naira miliyan 200 daga Shugaba Bola Tinubu da Stanley Osifo, waɗanda suka sayi fom ɗin neman takarar shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng


