2027: Jerin 'Yan Majalisar Tarayya 8 da Hana Su Takara a APC Ya Dauki Hankali a Arewa

2027: Jerin 'Yan Majalisar Tarayya 8 da Hana Su Takara a APC Ya Dauki Hankali a Arewa

KA makon da ya gabata ne jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta fara tsaida 'yan takararta na zaben 2027 ta hanyar sulhu kamar yadda ta tsara tun farko.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sai dai lamarin ya zo da wani yanayi da ba a yi tsammani ba domin sanatoci da 'yan Majalisar wakilai da dama sun rasa tikitin neman tazarce kan kujerunsu musamman a Arewacin Najeriya.

Shugaban APC na kasa.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda a ofishinsa da ke hedkwatar jam'iyya mai mulki a Abuja Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

APC ta amince da tsarin masalaha wajen takara

Tun farko APC ta zabi amfani da tsarin masalaha wajen tsayar da 'yan takararta kamar yadda ta sanar jadawalin zaben 2027 da ta wallafa a shafinta na manhajar X.

Wannan hanya da APC ta dauka ta jawo rudani da rigingimu iri daban-daban musamman daga wasu daga cikin wadanda suka nuna sha'awar neman takara a inuwar jam'iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi da bam ya fashe a Zamfara, an samu asarar rayuka

Dangane da batun 'yan takarar kujerun Majalisar tarayya, wasu daga cikin sanatoci da mambobin Majalisar wakilai sun rasa damar neman tazarce a wasu daga cikin jihohin Arewa.

Wasu 'yan majalisa da suka rasa tikitin takara

A wannan rahoton, mun tattaro muku yan Majalisar da rasa rasa tikitin da suka yi a APC ya dauki hankali a Arewacin Najeriya, ga su kamar haka.

1. Sanata Danjuma Goje

Sanatan Gombe ta Tsakiya, Danjuma Goje na cikin fitattun sanatocin Arewa da suka rasa tikitin APC bayan tsarin sulhu ya amince da DCP Mohammed Ahmadu Deba (Rtd) a matsayin 'dan takara.

Wannan mataki dai ya dauki hankali musamman bayan Sanata Goje, tsohon gwamnan jihar Gombe ya fito ya yi fatali da hakan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Danjuma Goje.
Sanata mai wakiltar Gombe ta Tsakiya a Majalisar dattawa, Ganduje Goje Hoto: Sen. Danjuma Goje Mohammed
Source: Facebook

Danjuma Goje, wanda ke neman wa'adi na biyar a Majalisar Dattawa, ya ce taron sulhu wanda Gwamna Inuwa Yahaya ya jagoranta, babu adalci a cikinsa domin ba a kira kowane mai neman takara ba.

2. Sanata Anthony Siyako Yaro

A watan Afrilun da ya gabata, Sanatan Gombe ta Kudu, Anthony Siyako Yaro, ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Da sake: Amnesty ta nemi a bi jinin matasan Kano da aka kashe bayan naɗa Garo

Sai dai duk da haka, a tsarin sulhun da APC ta aiwatar a Gombe, Sanatan ya rasa tikitin neman tazarce, inda jam'iyya mai mulki ta maye gurbinsa da Jery Damara a matsayin 'dan takara.

3. Sanata Nasiru Zangon Daura

Sanatan Katsina ta Arewa, Nasiru Sani Zangon Daura ya rasa tikicin tazarce a zaben 2027, inda APC ta yanke hukuncin tsayar da shugaban Majalisar dokokin jihar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura.

Nasir Yahaya ya samu nasarar zama 'dan takarara Sanatan Katsina ta Arewa ne a taron kwamitin sulhu da APC ta kafa, duk da dai an kai ruwa rana kafin cimma matsaya.

4. Hon. Abubakar Yahaya Kusada

Tsohon shugaban Majalisar dokokin jihar Katsina kuma dan Majalisar wakilai na mazabar Kankiya/Ingawa/Kusada, Rt. Hon Abubakar Yahaya Kusada ya rasa tikitin APC duk da dumbin ayyukan alherin da yake yi.

Kusada.
Dan Majalisar wakilai daga jihar Katsina, Hon. Abubakar Yahaya Kusada Hoto: Abubakar Yahaya Kusada
Source: Facebook

Kusada, wanda yana daya daga cikin yan Majalisar tarayya da ke kokarin samar wa matasa ayyuka gwamnati, ya rasa takara ne bayan kwamitin APC ya mika tikiti ga karamar hukumar Ingawa.

Dan Majalisar ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook, lamarin da ya ja hankalin jama'a matuka musamman a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

"Haka Allah ya tsara," 'Dan takarar APC, Jamilu Gwamna ya nemi hadin kan Pantami a Gombe

5. Hon. Sani Danlami

Hon. Sani Aliyu Danlami, mai wakiltar Katsina ta tsakiya a Majalisar wakilai ya rasa tikitin neman takara karo na uku a zaben 2027.

Jam'iyyar APC ta ba Abba Dahiru Mangal, dan fitaccen attajirin nan, Dahiru Mangal takarar kujerar Danlami, bayan tattaunawa mai zafi tsakanin mambobin kwamitin sulhu.

6. Hon. Aminu Jamo

Jam’iyyar APC mai mulki ta amince da Yusuf Buhari, 'dan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a matsayin ɗan takarar majalisar wakilai a mazabar Sandamu/Daura/Mai’adua.

Hakan na nufin ta hana dan Majalisa mai ci, Hon. Aminu Jamo tikitin sake neman takara bayan bai wa Yusuf Buhari, wanda wannan ne karo na farko da ya shiga siyasa.

Yusuf Buhari
Dan marigayi tsohon shugaban kasa, Yusuf Buhari yana magana lokacin da ya ziyarci Gwamna Dikko Radda a Katsina Hoto: Yusuf Buhari
Source: Twitter

7. Hon. El-Raseed Abdullah

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Gombe, Isma'ila Uba Misilli ya wallafa a Facebook, APC ta hana dan Majalisar wakilai na Dukku/Nafada, Hon. El-Raseed Abdullah tikitin neman tazarce.

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno kai, an tayar da hargitsi a wurin taron jam'iyyar NDC a Enugu

Maimakon haka, APC ta cimma matsaya tare da amincewa da Hon. Jamilu Shabewa a matsayin dan takararta na wannan mazaba a zaben da ke tafe.

8. Hon. Ahmad Yusuf

Hajiya Jamila Abdu Mani, wacce ta rike mukamin mai ba gwamna shawara kan ilimin ‘ya’ya mata, ta samu tikitin jam’iyyar APC ne ta hanyar tsarin sulhu a mazabar Mani da Bindawa, jihar Katsina.

Premium Times ta ce hakan ya sa ta doke dan majalisar wakilai mai ci, Hon. Ahmad Yusuf, da sauran masu neman takara. Lamarin ya ja hankali musamman kasancewarta mace.

Jamila Abdu Mani.
Yar takarar APC a kujerar majalisar wakilai ta mazbaar Mani da Bindawa, Hajiya Jamila Abdu Mani Hoto: Tijjani I. Jibrin
Source: Facebook

APC za ta tsaida dan takarar shugaban kasa

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta bayyana shirinta kan zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC babban zaɓen 2027 zai fito ne ta hanyar tsarin zaɓen fitar da gwani na kato bayan kato.

Bisa tanadin dokar zaɓe ta 2026, ’yan takara na muƙaman zaɓe za su iya fitowa ne ta hanyar zaɓen fitar da gwani na kato bayan kato ko kuma ta hanyar tsarin maslaha.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262