Atiku da Peter Obi Sun Tafka Kuskure, An Cire Su daga Barazanar da Tinubu Zai Fuskanta a 2027

Atiku da Peter Obi Sun Tafka Kuskure, An Cire Su daga Barazanar da Tinubu Zai Fuskanta a 2027

  • Sanata Orji Uzor Kalu ya ce Bola Tinubu ne ke kan gaba a hasashen wanda zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027
  • Ya ce Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran 'yan adawa sun yi kuskuren rashin hada kai, kuma ba za su iya kayar da Tinubu ba
  • Kalu ya ce jam'iyya mai mulki watau APC za ta ƙara ƙaimi wajen tallata ayyukan gwamnatin Tinubu kafin babban zaɓe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia, Nigeria - Sanatan da ke wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ke da mafi girman damar lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Sanata Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia, ya jaddada cewa jam’iyyun adawa sun yi rauni saboda rashin haɗin kai.

Orji Kalu.
Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu yana gabatar da kudiri a zaman Majalisar dattawa Hoto: Orji Uzor Kalu
Source: Twitter

Kalu ya bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya kare ayyukan gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Shugaba Tinubu zai lallasa 'yan adawa a zaben 2027'

Dan Majalisar dattawan ya ce duk da matsin tattalin arziki da ake fama da shi, gwamnati ta samu ci gaba wajen daidaita tattalin arziki da kuma inganta tsaro.

Kalu ya ce Tinubu ba shi da hamayya

Tsohon gwamnan jihar Abia ya ce babu wani ɗan takarar adawa da zai iya hana Tinubu sake komawa mulki a zabe mai zuwa.

Ya ce:

"Na faɗa a baya cewa Shugaba Tinubu ba shi da hamayya, kuma har yanzu ina nan kan wannan matsaya."

Ya ce irin nasarorin da gwamnatin ta samu da kuma ƙarfin APC a faɗin ƙasa sun sanya shugaban ƙasar cikin kyakkyawan matsayi gabanin zaɓen 2027.

Gwamnatin Tinubu ta gaza wajen tallata ayyukanta

Kalu ya bayyana cewa babban abin da ya rage wa gwamnatin Tinubu shi ne rashin tallata ayyukan da ta gudanar yadda ya kamata.

Sanatan ya ce idan za a tantance aikin shugaban ƙasar, zai ba shi maki 65 cikin 100.

Kara karanta wannan

Faston da ya buga da Tinubu a fadar shugaban kasa ya sake magana

"A cikin maki 100, zan ba Shugaba Tinubu maki 65. Matsalar da ta rage ita ce tattalin arzikin talakawa."

Ya ce Atiku da Obi ba barazana ba ne

Orji Kalu ya yi watsi da ra'ayin cewa Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran 'yan adawa za su iya kayar da Tinubu.

A cewarsa:

"Duk waɗannan mutane ba barazana ba ne. Da sun haɗa kai ne kawai za mu ɗan damu."

Ya ce rabuwar kan jam’iyyun adawa ita ce babbar fa'idar APC a shirye-shiryen zaɓen 2027, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Tonubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jagorantar taro a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956/X
Source: Twitter

Sanata Kalu na son APC ta karbi Abia

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Orji Kalu ya sha alwashin ganin jam'iyyar APC ta kwace mulkin jihar Abia a zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Sanata Orji Uzor Kalu ya yi alkawarin amfani da dukkan dukiyarsa domin taimaka wa jam’iyyar APC a zaben 2027.

Kalu ya ce zai mara wa Shugaba Bola Tinubu da dan takarar gwamnanna APC baya, yana mai jaddada cewa zai sa zuciyarsa gaba daya a yakin neman nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262