An Fara Jita Jitar Cewa Sheikh Abdulmudallib Ya Samu Tikitin Takarar Gwamna a 2027
- An fara yada jita-jitar cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta tsayar da Sheikh Abdulmudallib Muhammad takarar gwamnan Zamfara a 2027
- Duk da ba wata sanarwa a hukumance, an ce fitaccen malamin addinin musulunci ya samu tikiti bayan amincewar shugabanni da mambobin ADC
- Ana sa ran takararsa za ta kara zafafa fafatawar siyasa a jihar yayin da Gwamna Dauda Lawal ke neman tazarce a inuwar jam'iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun nuna cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Abdulmudallib MuhammaD, ya samu tikitin takarar gwamna na ADC a Zamfara.
Jita-jitar ta nuna cewa jam’iyyar ta amince da malamin ne bayan tuntubar shugabanni, masu ruwa da tsaki da kuma mambobin jam’iyyar a fadin jihar da ke Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Jam'iyyar APC ta dakatar da dan majalisar tarayya daga jihar Jigawa

Source: Facebook
Kafar watsa labarai ta Freedom Radio Nigeria ta bayyana hakan a wani gajeren sako da ta wallafa a shafin Facebook yau Laraba, 3 ga watan Yuni, 2026.
Jita-jitar takarar Sheikh Abdulmudallib
An ruwaito cewa shugabannin jam’iyyar ADC sun bayyana cewa an zabi Sheikh Abdulmudallib Auwal ne saboda irin gudunmawar da yake bayarwa wajen wayar da kan al'umma da kuma kyakkyawan suna da yake da shi a tsakanin jama'a.
Sun ce jam’iyyar na da yakinin cewa dan takararta zai iya jan hankalin masu kada kuri’a daga bangarori daban-daban na jihar, musamman matasa da masu neman sauyi a harkokin shugabanci.
Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga jam'iyyar ADC ko malamin, da ta tabbatar da wadannan rahotanni da jita-jita da ake yadawa.
Yadda zaman sulhun ADC ya gudana
Wasu rahotanni sun nuna cewa a zaman sulhu da aka yi tsakanin masu neman tikitin jam'iyyar ADC domin cimma matsaya ta hanyar masalaha ba tare da an yi zabe ba.
Masu neman takarar gwamna a inuwar ADC a Zamfara sune Malam Shehu Isa (Bardej Gusau), Mahdi Aliyu Gusau, Barista Bello Galadi, Sheikh Abdulmudallib Auwal Gusau da Sulaiman Tukur.
Wasu bayanai sun nuna cewa shugabanbin ADC sun amince da tsohon mataimakin gwamna, Mahdi Aliyu Gusau a matsayin dan takarar gwamna.

Source: Facebook
An ce tun farko, masu ruwa da tsakin ADC sun cimma matsayar cewa za a dauki dan takarar gwamna daga yankin Zamfara ta Tsakiya, domin ba su damar shugabanci da bin tsarin daidaito.
To sai dai jita-jitar cewa ADC ta tsaida Sheikh Abdulmudallib takarar gwamnan Zmafara ta haifar da rudani game da batun takarar Mahdi Aliyu Gusau.
Rikici ya barke a ADC a Adamawa
A wani labarin, kun ji cewa tsugunne ba ta kare ba a jam'iyyar ADC reshen jihar Adamawa biyo bayan kammala zaben fitar da gwani don zabar 'yan takara.
Rahotanni sun nuna cewa wani sabon rikici ya ɓalle a cikin jam'iyyar ADC a Jihar Adamawa sakamakon zargin da ake yi kan tafka magudi a zaben da aka kammala.
Ana dai zargin cewa ana tafka magudi a kan sakamakon zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar ADC na Majalisar wakilai na Mazabar Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da Girei.
Asali: Legit.ng
