Abin da Zai Faru a Jam'iyyar APC idan Aka Gaza Samun Ɗan Takara Ta Hanyar Sulhu
- Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana cewa jam’iyyar APC a Jihar Yobe za ta yi zaben ƙato bayan ƙato idan har ba a cimma matsayar bai-daya kan dan takara ba
- Masu neman takarar gwamna shida sun yi watsi da zaman sulhu da wasu jiga-jigan jam’iyyar suka yi na tsayar da Alhaji Baba Wali matsayin ɗan takara
- Gwamnan ya nanata cewa hadin kan jam’iyyar shi ne babban burinsa, kuma za su ci gaba da tattaunawa da wadanda zabin Wali bai yi wa daɗi ba don neman mafita
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Yobe - Gwamnan Yobe Mai Mala Buni, ya bayyana cewa jam’iyyar APC tana da kudirin gudanar da zaben ƙato bayan ƙato idan har ba a samu daidaito kan tsayar da dan takara ta hanyar sulhu ba.
Wannan bayani yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Darakta Janar na yada labarai na gwamnan, Mamman Mohammed, ya fitar a Damaturu ranar Lahadi.

Source: Twitter
Yobe: Ƴan takara 6 sun yi watsi da sulhu
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wasu masu neman takarar gwamna shida sun ki amincewa da Alhaji Baba Wali, a matsayin dan takarar sulhu na jihar.
Masu neman takarar sun hada da:
- Sanata Ibrahim Bomoi (Yobe ta Kudu)
- Alhaji Bashir Machina
- Malam Kashim Musa-Tumsah
- Malam Mustapha Maihaja
- Alhaji Lawan Kolo
- Mohammed Baba (Tsohon Sufeto Janar na Yan Sanda)
Buni: 'Ba mu sauya tsarin zabe ba'
Gwamna Buni ya jaddada cewa jam’iyyar ba ta soke tsarin gudanar da zabe kai-tsaye ba, watau ƙato bayan ƙato domin samar da yan takara a zaben 2027.
Ya bayyana cewa:
“Tsayar da Mallam Wali a matsayin wanda jam’iyya ta fi so ya biyo bayan kudurin taron jiga-jigan jam’iyya na ranar 23 ga Afrilu, 2026. Idan har ba a samu amincewar kowa ba, za mu koma ga tsarin zabe na ƙato bayan ƙato.
"Wannan ba sabon abu ba ne; a 2019 an zabe ni ta hanyar daidaito, amma wasu suka nuna rashin amincewa, aka tafi zaben ƙato bayan ƙato inda na yi nasara da gagarumin rinjaye.”
Gwamnan ya kara da cewa har yanzu jam’iyyar tana tuntubar masu neman takarar da ke jin haushi domin nemo maslaha ta hanyar tattaunawa cikin lumana.

Source: Original
Burin APC ga zaben 2027
A matsayinsa na tsohon sakatare kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Buni ya ce hadin kai da ci gaban jam’iyyar suna da muhimmanci a gare shi.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa burin kowane dan takara shi ne ya bauta wa jama’a domin inganta rayuwarsu.
Daga karshe, Gwamna Buni ya ba da tabbacin cewa jam’iyyar za ta bai wa kowa damar baje kolinsa, kuma za ta marawa duk wanda ya fito a matsayin dan takara baya domin APC ta lashe zaben shugaban kasa, gwamna, da dukkan kujerun majalisun jiha da na kasa a Jihar Yobe.
Asali: Legit.ng

