Jamila Abdu Mani: Mace Ta Tika Namiji da Kasa, Ta Lashe Tikitin Takarar APC a Jihar Katsina
- Mace daya tilo da ta fito neman takara a jihar Katsina, Hajiya Jamila Abdu Mani ta samu nasarar zama yar takarar Majalisar wakilai a inuwar APC
- Hakan ya biyo bayan kammala zaben fitar da gwani da jam'iyyar APC ta gudanar a mazabar Mani da Bindawa a yau Asabar
- Hajiya Jamila ta samu nasarar lashe tikitin APC ne bayan doke abokin hamayyarta, Ahmed Saleh da kuri'u 24,989
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Jamila Abdu Mani, wadda ita ce mace daya tilo da ta tsaya takara a jihar Katsina, ta samu nasarar lashe tikitin takarar Majalisar wakilai.
Hajiya Jamila, tsohuwar mai ba gwamnan Katsina shawara kan ilimin mata, ta lashe tikitin jam’iyyar APC na mazabar Bindawa/Mani ta tarayya a zaben shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan
Mahmud Buba: Abin Al'ajabin Zazzau ya janye daga neman takarar dan majalisar wakilai

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kwamitin gudanar da zaben fitar da gwani na mazabar, Shaif’u Audu-Duwan, ne ya sanar da sakamakon bayan kammala kada kuri'a a ranar Asabar a karamar hukumar Mani.
Jamila Abdu Mani ta samu tikitin APC
A cewarsa, sakamakon da aka tattara daga gundumomi 22 ya nuna cewa Hajiya Jamila ta samu kuri’u 24,989, yayin da abokin takararta, Ahmed Saleh, ya samu kuri’u 1,256.
Shafi'u Audu-Duwan ya ce:
“An gudanar da zaben fitar da gwani a mazabar Bindawa/Mani ne saboda tsarin maslaha bai yi nasara ba, ganin cewa ‘yan takara biyu sun nuna sha’awar tsayawa takara.
“Saboda rashin cimma matsaya a kan maslaha, ‘yan takarar biyu suka amince a shiga zaben fitar da gwani, kuma Jamila Abdu Mani da ta samu mafi yawan kuri’u an ayyana ta a matsayin wadda ta yi nasara.
"Don haka yanzu ita ce ‘yar takarar APC ta mazabar Mani/Bindawa ta tarayya. Wannan ya nuna cewa APC na hade, kuma za mu yi aiki domin nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa."
Hajiya Jamila ta yi jawabin godiya
Da take jawabin godiya bayan kammala zaben, Hajiya Jamila ta gode wa al’ummar mazabar bisa ba ta damar tsayawa takarar Majalisar wakilai ta kasa.
Ta kuma yabawa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda, da shugabannin APC a jihar saboda ba ta damar shiga zaben fitar da gwani, kamar yadda Premium Times ta kawo.

Source: Facebook
Jamila Mani ta roki al’ummar mazabar, musamman mata, da su zabe ta a babban zaben 2027 domin ta samu damar wakiltar muradunsu a Majalisar Tarayya.
“Da ikon Allah, idan aka zabe ni a matsayin ‘yar majalisar wakilai, zan yi amfani da gogewata wajen wakiltar mazabata yadda ya kamata," in ji ta.
An fara sukar takarar mace a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa malaman addinin musulunci sun yi fatali da matakin tsaida mace a matsayin 'yar takarar kujerar Majalisar wakilai a mazabar Mani da Bindawa.
Wani malami mai suna, Malam Abu Abdullahi yabayyana rashin jin dadinsa, yana mai cewa bai dace a ba mace shugabanci ba bisa koyarwar hadisai.
Sai dai kwamandan rundunar Hisbah na jihar Katsina, Abu Ammar, ya taba bayyana cewa Musulunci bai hana mata rike mukaman shugabanci ba,
Asali: Legit.ng
