Kwana 3 kafin Zabe, INEC Ta Ƙara Sunan Dan Takara 1 a Zaben Gwamnan Jihar Osun

Kwana 3 kafin Zabe, INEC Ta Ƙara Sunan Dan Takara 1 a Zaben Gwamnan Jihar Osun

  • Hukumar INEC ta ƙara Dr Francis Olugbenga Ajala da abokin takararsa Faseke Babajimi Oladipo a cikin takardar zaɓen gwamnan Osun
  • INEC ta ɗauki wannan matakin ne domin biyayya ga hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Abuja
  • Ƙarin SDP ya sa yawan jam’iyyun da za su fafata a zaɓen gwamnan Osun ranar Asabar mai zuwa ya koma 15

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ƙara ɗan takarar jam’iyyar SDP), Dr Francis Olugbenga Ajala, da abokin takararsa, Faseke Babajimi Oladipo, a takardar zaɓen gwamnan jihar Osun na 2026.

INEC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Kwamishinanta na Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya fitar ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Dan takarar NDC: 'Abin da ya sa Najeriya ke bukatar Obi da Kwankwaso'

INEC.
Tambarin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Me ya sa INEC ta ƙara SDP?

A rahoton Leadershi, hukumar ta ce matakin ya biyo bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke ranar 22 ga Yuli, 2026, a cikin ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/344/2026.

Ƙarar ta shafi SDP, Ajala da INEC, inda kotun ta umarci hukumar da ta amince da Ajala a matsayin ɗan takarar jam’iyyar na zaɓen gwamnan Osun.

Hukuncin ya kuma umarci INEC da ta karɓi, loda, sarrafa tare da wallafa sunan Ajala da sauran bayanan da suka shafe shi a matsayin ɗan takarar SDP.

Bayan hukuncin, INEC ta ce ta fara sake buga takardun zaɓen domin saka sunan Ajala da kuma tabbatar da cewa bayanan zaɓen sun dace da sabon sauyin.

Jam’iyyu 15 za su fafata a Osun

INEC ta ce an kuma fara sake buga takardun sakamakon zaɓen tare da takardun zaɓe domin su kasance da sunan ɗan takarar SDP.

Kara karanta wannan

Atiku ya dura Osun, ya bukaci a murkushe APC da dan takarar ta

Da ƙarin SDP cikin jerin masu neman kujerar gwamna, INEC ta ce adadin jam’iyyun siyasar da za su fafata a zaɓen gwamnan Osun ya kai 15.

Amupitan.
Shugaban hukumar INEC ta kasa, Farfesa Joash Amupitan yana jawabi a taro Hoto: @INECNigeria
Source: Twitter

Za a gudanar da zaɓen ne ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026, inda masu zaɓe a jihar za su fito domin zaɓar wanda zai jagorance su na tsawon shekaru hudu masu zuwa

Hukumar ta ce ana sa ran sabbin takardun zaɓen da aka sake bugawa za su isa jihar Osun ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, kamar yadda Vanguard ta kawo.

A cewar INEC, da zarar takardun sun isa Osun, za a rarraba su zuwa ofisoshin hukumar na ƙananan hukumomin jihar a wannan rana.

Alkawarin da Tinubu ya yi kan zaben Osun

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kira shi da kansa lokacin da EFCC ta rufe asusun gwamnatin jihar Osun.

Gwamna Adeleke ya bayyana cewa shugaban kasar ya yi masa alkawarin gudanar da zabe cikin ’yanci da adalci, ba tare da tashe-tashen hankula ba.

Bayan Adeleke ya bayyana kiran na Tinubu, sakonsa ya jawo martani daga ’yan Najeriya da dama a kafafen sada zumunta, inda wasu suka nuna shakku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262