"Kamar Nadin Sarauta," Masani Ya Yi Kaca Kaca a Nasarar da Tinubu Ya Samu a APC
- Masana sun fara tofa albarkacin bakinsu kan zaben fitar da dan takarar shugaban kasa da jam'iyyar APC ta gudanar
- Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara da gagarumin rinjaye, inda ya tika dan kasuwa, Stanley Osifo da kasa a zaben
- Jide Ojo, wani mai sharhi kan harkokin yau da kullum ya ce zaben fidda gwanin APC ya yi kama da nadin sarauta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Masanin harkokin jama’a na yau da kullum, Jide Ojo, ya soki zaben fitar da gwanin jam'iyyar APC na shugaban kasa, wanda aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.
Mista Ojo ya kwatanta zaben, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara,da 'nadin sarauta', yana mai cewa babu wata gwabzawa ta hakika da aka yi a zaɓen.

Source: Facebook
Ojo ya bayyana hakan ne a shirin The Morning Brief na Channels TV ranar Litinin yayin da yake martani kan zaɓen fitar da gwani na APC da aka gudanar a mazaɓu 8,809 da ke jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Masani ya soki zaben ftar da gwanin APC
A cewarsa, tun farko alamu sun nuna cewa an riga an tsara sakamakon zaɓen, yana mai cewa da jam’iyyar ta ɗauki lokaci sosai wajen shirya zaɓen, da an samu gasa mai ma’ana.
“Ina ganin cewa wannan zabe da aka yi tamkar naɗin sarauta ne kawai, dauka aka yi aka dora, an riga an taara komai tun farko.
"Wani mutum ya kashe Naira miliyan 100 sannan ya samu ƙuri’u 16,503 kacal, a jihohi 21 bai samu ko ƙuri’a ɗaya ba, a jiharsa ta Edo ya samu ƙuri’a ɗaya ne kawai,” in ji shi.
Ojo na magana ne kan ɗan kasuwa kuma tsohon mamban PDP, Stanley Osifo, wanda ya fafata da Shugaba Bola Tinubu bayan sayen fom ɗin takarar shugaban ƙasa na APC kan kudi Naira miliyan 100.
Tinubu ya lashe zaɓen da jimillar ƙuri’u miliyan 10.9, yayin da Osifo ya samu ƙuri’u 16,503, kamar yadda Leadership ta kawo.

Source: Twitter
Ojo ya yi sharhi kan takarar Osifor
Sai dai Ojo ya ce Osifo na da cikakken ‘yancin shiga takarar kuma ya kara da Shugaba Tinubu komai kankantar sakamakon da ya samu.
“Wasu na cewa ɗaukar nauyinsa aka yi, amma babu wata hujja da ta tabbatar da hakan. Abin da muka sani shi ne ɗan kasuwa ne, ya kashe Naira miliyan 100 nasa, kuma yau mutane na magana a kansa.
“Ya saka sunan iyalinsa a taswirar siyasar Najeriya idan ana maganar zaɓen 2027," in ji shi,.
Masanin ya ƙara da cewa shiga takarar da Osifo ya yi zai ci gaba da zama wani ɓangare na tattaunawar siyasar Najeriya yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Shin Tinubu ya cancanci wa'adi na 2?
A wani labarin, kun ji cewa ministan lafiya, Muhammad Ali Pate ya yi bayanin abin da ya sa yake ganin Shugaba Bola Tinubu ya cancanci tazarce a zaben 2027.
Ministan ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya cancanci yan Najeriya su sake zaɓensa karo na biyu duba da nasarorin da gwamnatinsa ta samu a shekara uku.
Ali Pate ya ce daga cikin nasarorin gwamnatin Bola Tinubu har da samar da aikin yi ga matasa sama da 3,000 a Jihar Bauchi.
Asali: Legit.ng


