Matar da APC Ta Tsaida Takara a Katsina Ta Fara Fuskantar Cikas daga Malaman Musulunci
- Malaman addinin musulunci sun yi fatali da matakin tsaida mace a matsayin 'yar takarar kujerar Majalisar wakilai a mazabar Mani da Bindawa
- Sun bayyana cewa musulunci ya hani al'umma dora mata a matsayin shugabanni, inda suka yi kira ga jama'a da kar su zabe ta
- Sai dai kwamandan Hisbah na Katsina, Sheikh Abu Ammar yana da fahimtar da ta saba wa wannan kan batun shugabancin mata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina – Wasu malaman addinin Musulunci a kananan hukumomin Mani da Bindawa na jihar Katsina sun bukaci al’umma da kada su zabi Jamila Abdu-Mani, ‘yar takarar APC a zaben majalisar wakilai na 2027.
Hajiya Jamila, wacce ta rike mukamin mai ba gwamna shawara kan ilimin ‘ya’ya mata, ta samu tikitin jam’iyyar APC ne ta hanyar tsarin sulhu, inda ta doke dan majalisa mai ci, Hon. Ahmad Yusuf, da sauran masu neman takara.

Kara karanta wannan
Poland ta magantu da sojan Isra'ila ya sa wa mutum mutumin mamar Yesu sigari a baki

Source: Facebook
Malamai sun nuna rashin amincewa
Premium Times ta ce wani malami mai suna, Malam Abu Abdullahi ya bayyana rashin jin dadinsa, yana mai cewa bai dace a ba mace shugabanci ba bisa koyarwar hadisai.
Ya ce:
“Manzon Allah (SWA) ya gargade mu game da bai wa mata shugabanci. Me ya sa za mu kauce wa koyarwar addinin mu?”
Haka kuma wani malami a Bindawa, Usman Salisu, ya bukaci shugabannin yankin da su kalubalanci matakin zaben ‘yar takarar jam'iyya mai mulki, yana mai cewa hakan ya saba da ka’idojin Musulunci.
Abu Ammar ya saba wa fahimtarsu
Sai dai kwamandan rundunar Hisbah na jihar Katsina, Abu Ammar, ya taba bayyana cewa Musulunci bai hana mata rike mukaman shugabanci ba, matukar ya dace da dabi’u da al’adun al’umma.
Malamim musuluncin ya ce mata na da damar rike mukamai idan hakan bai saba da ka’idojin zamantakewa da tarbiyya ba.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa mutane wuta a wurin jana'iza a Filato
Tarihin mata a siyasar Katsina
Duk da cewa mata sun taba rike mukaman gwamnati a jihar Katsina, samun nasara a zabuka ya kasance kalubale saboda rashin yawan tsayar da su takara daga manyan jam’iyyu.

Source: Facebook
A shekarar 1991, Mariya Abdullahi ta taba lashe zaben majalisar wakilai a yankin Bakori/Danja, yayin da Hadiza Bala Usman ta tsaya takara a 2011 amma ba ta yi nasara ba.
Hadiza Bala Usman ta tsaya a CPC domin wakiltar mutanen Musawa da Matazu a Majalisar tarayya.
Haka kuma, wasu kananan hukumomi kamar Mani, Bakori, Dutsin-Ma da Kurfi sun taba samun shugabanni mata a lokuta daban-daban, kamar yadda Daily Post ta kawo.
Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan wannan lamari, wani dalibin ilimi, Malam Yahuza ya shaidawa Legit Hausa cewa bai halatta mata su rike kujerun shugabanci ba a musulunci.
Ya ce akwai manyan malamai magabata da suka yi rangwame a wasu wuraren, amma kujeru irinsu gwamna, shugaban kasa, da sauran zababbu bai kamata a zabi mace ba.

Kara karanta wannan
"Haka Allah ya tsara," 'Dan takarar APC, Jamilu Gwamna ya nemi hadin kan Pantami a Gombe
"Maganar shugabancin mace a al'umma magana ce babba, to sai dai yanzu wasu malaman na bada fatawowi masu cin karo da juna, wasu na ganin mukamin da ya shafi mata zalla, ba wani abu ba ne dan an ba mace," in ji shi.
APC ta bai wa 'dan Mangal takarar Majalisa
Awani labarin, kun ji cewa Hon. Sani Aliyu Danlami, mai wakiltar Katsina ta tsakiya a Majalisar wakilai ya rasa tikitin neman takara karo na uku a zaben 2027.
Danlami, wanda ke wa’adinsa na biyu a majalisar wakilai, ya sha kaye ne bayan tattaunawa mai zafi da aka shafe kwanaki ana yi tsakanin manyan jiga-jigan APC da kwamitin sulhu na mazabarsa.
Kwamitin sulhu da Gwamna Dikko Radda ya kafa, ya amince da Abba Mangal, daya daga cikin ’ya’yan fitaccen attajiri, Dahiru Mangal, a matsayin dan takarar APC a mazabar Katsina ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng