NDC: Jam'iyyar Su Obi Ta Rikice kan Zaɓen Fitar da Gwani a Jihar Delta

NDC: Jam'iyyar Su Obi Ta Rikice kan Zaɓen Fitar da Gwani a Jihar Delta

  • Dan takarar kujerar Majalisar Wakilai a jam’iyyar NDC, Julius Akbovoka, ya bukaci a gudanar da adalci wajen tantance sakamakon zaben fitar da gwani a jihar Delta
  • Ya ce har yanzu bai samu sanarwar hukuma daga jam’iyyar kan sakamakon zaben ba, yana zaman jiran halin da ake ciki bayan ya shiga an fafata da shi a neman takara
  • Akbovoka ya yi ikirarin cewa shi ne ya samu mafi yawan kuri’u a rumfunan zaben da aka gudanar saboda haka yana dakon a sanar da shi a hukumance halin da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Delta - Dan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a karkashin jam’iyyar NDC mai wakiltar mazabar Ughelli North/Ughelli South/Udu a jihar Delta, Julius Akbovoka, ya rubuta koke ga kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Jam'iyyar APC ta dakatar da dan majalisar tarayya daga jihar Jigawa

Akbovoka ya bukaci shugabannin jam’iyyar su tabbatar da gaskiya da adalci wajen kula da sakamakon zaben fitar da gwani da aka gudanar domin fitar da ‘yan takara.

Mai neman takara a Delta ya rubuta wasika ga shugabannin NDC
Jagorori a NDC, Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa da yake ganawa da manema labarai a Abuja ranar Talata, 2 ga watan Yuni, 2026, ya ce ya kamata sakamakon da aka samu daga cibiyoyin kada kuri’a daban-daban ya kasance abin da za a yi amfani da shi wajen fitar da sakamakon karshe.

Mai neman takara a NDC ya koka

Jaridar Leadership ta kawo labarin cewa konen Akbovoka na zuwa ne bayan jam’iyyar NDC ta nesanta kanta daga wasu sakamakon zabukan fitar da gwani da suka yadu a kafafen sada zumunta.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Osa Director, ya fitar a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu, 2026 ya bukaci jama’a su yi watsi da sakamakon da ake yadawa.

Ya jaddada cewa kwamitin gudanarwa na kasa ne kadai ke da ikon sanar da sakamakon zabukan fitar da gwani da aka gudanar tsakanin ranar 28 zuwa 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Zaben fitar da gwani: Diyar Tinubu ta yi barazanar jagorantar zanga zanga a APC

Ana son a yi adalci a NDC

Dan takarar ya bayyana cewa ya yanke shawarar yin jawabi ga manema labarai ne saboda har yanzu bai samu wata sanarwa a hukumance daga jam’iyyar game da sakamakon zaben ba.

Ya ce ya shiga jam’iyyar NDC ne a ranar 30 ga Afrilu, 2026 kuma ya taka rawar gani a ayyukan jam’iyyar, daga ciki har da babban taro da rajistar 'ya'yanta.

Dan takarar NDC na naeman a saki sakamakon zabe
Shugabannin NDC, Peter Obi, Seriake Dickson, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Seriake Henry Dickson
Source: Twitter

Akbovoka ya ce:

“Ba na neman a canza alkaluma domin amfanina. Abin da nake bukata shi ne a sake duba sakamakon da aka samu tare da aiwatar da shi bisa dokoki da ka’idojin jam’iyya.”

Dan majalisa ya bar NDC

A baya, kun samu labarin cewa dan Majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazabar Makoda, Muhammad Ahmad Tomas ya sauya sheka daga NDC zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya karbe shi a wata ziyara daya kai masa har gida a Abuja ramar Litinin, 1 ga watan Yuni 2026 inda ya tabbatar da sauya shekarsa.

Sanata Barau I Jibrin ya tabbatar wa dan ajalisar cewa za a ba shi cikakkiyar dama kamar yadda kowane mamba ke samu a APC ya ke samu ba tare da an nuna wariya tsakaninsa da tsofaffin yan jam'iyya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng