Shugaban Amurka Donald Trump ya ce hare-haren da kasarsa ke kaiwa Iran za su ci gaba, yana mai jaddada cewa ba za a bari Tehran ta mallaki makamin nukiliya ba.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce hare-haren da kasarsa ke kaiwa Iran za su ci gaba, yana mai jaddada cewa ba za a bari Tehran ta mallaki makamin nukiliya ba.
Tsohon mataimakin gwamnan Kebbi, Ibrahim Aliyu, ya rasu bayan rashin lafiya. Gwamna Nasir Idris ya yi jimamin rasuwarsa tare da yabawa gudummawar da ya bayar.
A kalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu bayan ‘yan sanda suka biyo da babbar mota dankare da amfanin gona. Babbar motar ta murkushe Keke Napep masu yawa a ranar ranar Talata.
Wata mata 'yar kasar Bangladesh mai yin aiki a wani gida a kasar Saudi Arabia ta fitar da wani faifan bidiyo mai cike da al'ajabi inda take bukatar taimako. A bidiyon ta zargi ubangidanta da cin zarafinta kuma ta bukaci tallafin..
Kotun daukaka kara da ke zama a Calabar a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba ta tabbatar da nasarar Udom Emmanuel a matsayin zababben gwamnan jihar Akwa Ibom.
Kwararre a fannin zamantakewa, Joro Olumofin ya bayyana wani sako da wata mata ta aika masa ta yanar gizo. A sakon matar ta bayyana cewa ta fi son mijinta idan bashi da kudi...
Hukumar yan sandan jihar Kaduna ta saki shahrarren dan kasuwa kuma tsohon shugaban kamfanin motar Peugeot Automobile Nigeria Ltd., PAN, Alhaji Sani Dauda ASD, bayan an tsareshi kan aurar da diyarsa, Daily Nigerian ta ruwaito.
Fitacciyar jarumar nan ta masana'antar Nollywood mai dirarriyar sura wato Moyo Lawal, ta mayar da martani akan wata magana da masoyanta suka yi a kanta. Biyo bayan wallafa wasu hotuna a shafukanta na sada zumunta da suke nuni da..
Gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da aikin tantancewa tare da yi ma bakin haure mazauna jahar Sakkwato rajista tare da hadin gwiwar hukumar kula da shige da fice ta Najeriya.
Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kammala aikin titin daya tashi daga Abuja zuwa birnin Algiers na kasar Algeria.
Dakarun rundunar Sojan saman Najeriya sun yi amfani da jiragen yaki wajen ragargazan mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a wani samame da suka kai musu yayin da suka taru a sansanoninsu a yankin tafkin Chadi.
Labarai
Samu kari