An Yi Babban Rashi: Tsohon Mataimakin Gwamna a Arewacin Najeriya Ya Kwanta Dama
- Tsohon mataimakin gwamnan Kebbi, Ibrahim K. Aliyu, ya rasu bayan doguwar jinya, lamarin da ya girgiza iyalansa da al'ummar jihar
- Gwamna Nasir Idris ya bayyana rasuwar Aliyu a matsayin babban rashi ga Masarautar Yauri, Jihar Kebbi da Najeriya baki daya
- Gwamnan ya jajanta wa iyalan marigayin, ya roƙi Allah ya gafarta masa, ya ba shi Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansa hakurin jure rashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Kebbi - Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Ibrahim K. Aliyu, ya rasu.
Marigayin, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Yauri a jihar Kebbi, ya rasu ne a wani asibiti da ke jihar Sokoto bayan ya shafe lokaci yana fama da rashin lafiya.

Source: Facebook
Tsohon mataimakin gwamna ya rasu
An bayyana cewa ya bar kyakkyawan tarihi na riƙon amana, jajircewa da kuma hidimar jama'a, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya nuna.
Da yake mayar da martani kan rasuwar, gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya ce mutuwar Ibrahim K. Aliyu ta yi wa jihar Kebbi rashin ɗaya daga cikin fitattun shugabanninta masu mutunci, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al'umma hidima cikin gaskiya da riƙon amana.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kai, Yahaya Sarki, ya fitar.
Gwamnan Kebbi ya yi alhinin rasuwar
A cikin sanarwar, gwamnan ya bayyana rasuwar tsohon mataimakin gwamnan a matsayin babban abin baƙin ciki da kuma rashi da ba za a iya cike gibinsa ba ga masarautar Yauri, jihar Kebbi da Najeriya baki ɗaya.
Ya ce:
"A madadin gwamnatin jihar Kebbi da al'ummar jihar baki ɗaya, ina miƙa ta'aziyyata ga iyalan marigayin, al'ummar masarautar Yauri, abokansa, masu hulɗa da shi da kuma duk waɗanda wannan rashi ya shafa.
"Muhimman gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa jiharmu da jajircewarsa wajen kyautata rayuwar al'umma za su ci gaba da zama abin koyi ga tsararraki masu zuwa."
An tuno hidimar tsohon gwamnan Kebbi
Sanarwar ta ƙara da cewa za a ci gaba da tunawa da marigayin ba kawai saboda irin nasarorin da ya samu a siyasa ba, har ma saboda ƙwarewa da sadaukarwar da ya nuna a aikin gwamnati, wanda ya sa ya samu girmamawa daga mutane da dama.
Gwamna Nasir Idris ya kuma roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayin, Ya sa ya huta a Aljannatul Firdaus.
Hakazalika, ya sake miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, masarautar Yauri da daukacin al'ummar jihar Kebbi, tare da addu'ar Allah Ya ba su haƙurin jure wannan babban rashi.
Asali: Legit.ng

