Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana kan Ƙarin Kuɗin Wutar Lantarki a Najeriya

Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana kan Ƙarin Kuɗin Wutar Lantarki a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta ce ba ta da shirin ƙara kuɗin wutar lantarki a yanzu, tana mai jaddada aniyarta ta inganta samar da wuta ga 'yan Najeriya
  • Ministan wutar lantarki ya ce gwamnati na ƙarfafa gyare-gyare, zuba jari da shirin saka mitoci domin tabbatar da adalci da inganta samar da wutar
  • Gwamnati ta ƙaddamar da shirin daukar matasa 5,000 aikin saka mitoci, tare da bayyana cewa samar da wuta ya zarce megawatt 5,000 kwanan nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba ta da wani shiri na ƙara kuɗin wutar lantarki a wannan lokaci, tana mai jaddada aniyarta ta inganta samar da wuta ta hanyar gyare-gyare da zuba jari a fannin makamashi.

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Legas.

Kara karanta wannan

Hukumar makaranta ta hango babbar matsala, an dakatar da karatu a jami'ar Jos

Gwamnati ta yi bayani kan gyaran fannin wutar lantarki

Ya ce taron ya zama farkon wani sabon babi na buɗe ƙofa, riƙon amana da haɗin gwiwa a fannin wutar lantarki, yayin da gwamnati ke ƙara ƙaimi wajen samar da ingantacciyar wuta mai ɗorewa ga 'yan Najeriya a ƙarƙashin Ajandar Renewed Hope.

Joseph Tegbe ya ce gyaran da ake yi wa fannin wutar lantarki ba yana nufin yin watsi da nasarorin da aka samu a baya ba.

Ya ce manufar ita ce gina kan sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fara, tare da magance matsalolin da suka daɗe suna hana fannin bunƙasa.

Ya ce:

"Manufarmu a bayyane take, ita ce tabbatar da samun wutar lantarki cikin sauƙi, inganta tsarin rarraba wuta, tabbatar da dorewar kasuwar wutar lantarki da kuma dawo da amincewar masu zuba jari. Burinmu shi ne wutar lantarki ta zama ginshiƙin bunƙasar tattalin arziki."

Gwamnati ta musanta shirin ƙara kuɗin wuta

Kara karanta wannan

Minista ya cire tsoro, ya fadi babban abin da ke rura wutar ta'addanci a Najeriya

Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya nuna ƙuduri wajen aiwatar da sauye-sauye a fannin wutar lantarki, yana mai cewa babu wata ƙasa da za ta bunƙasa masana'antu ba tare da ingantacciyar wuta ba.

Da yake magana kan rahotannin da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai, Tegbe ya ce gwamnatin tarayya ba ta da wani shiri na ƙara kuɗin wutar lantarki a yanzu.

Ya ce gwamnati na mayar da hankali ne wajen faɗaɗa samun wutar lantarki da kuma tabbatar da adalci ga masu amfani da ita ta hanyar Shirin Saka Mita na Shugaban Ƙasa (Presidential Metering Initiative), wanda ke ƙoƙarin tabbatar da cewa kowane mai amfani da wuta ya samu mita.

Gwamnati ta ƙaddamar da sabon shiri

Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati na ci gaba da zuba jari wajen inganta layukan wutar lantarki, faɗaɗa samar da wuta a karkara da kuma jan hankalin masu zuba jari masu zaman kansu.

Daga cikin sabbin matakan da ma'aikatar ta ƙaddamar akwai shirin Power Force, wanda zai ɗauki matasa 'yan Najeriya 5,000 aikin saka mitoci a faɗin ƙasar ta hannun Cibiyar Horar da Ma'aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NAPTIN).

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta lallaba Saudiyya, tana so a taimaka wa Najeriya kan karatun allo

Ana sa ran shirin zai taimaka wajen rage ƙarancin mitoci tare da samar da ƙwararrun ma'aikata a fannin wutar lantarki.

Ministan ya kuma ƙara da cewa samar da wutar lantarki ya inganta, inda tsarin wutar lantarki na ƙasa ya rika samar da fiye da megawatt 5,000 a cikin makonni biyu da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com