Aure a kan aure mata ta za ta yi - Surukin ASD ya kare kansa

Aure a kan aure mata ta za ta yi - Surukin ASD ya kare kansa

Abubakar Musa, sirikin babban dan kasuwar nan na jihar Kaduna, Sani Dauda ya warware abinda ke tsakaninsa da sirikinsa da yasa har jami'an 'yan sanda suka cafkesa.

Idan zamu tuna, a ranar Talata da karfe 4 na yammaci, jami'an SARS da ke aiki da hukumar 'yan sandan jihar Kaduna sun kama Sani dauda tare da dansa , Murtala Nasir, alkali a kotun shari'a ta jihar Kaduna da sabon sirikinsa Abdullahi Kumali.

An gano cewa, 'yan sandan na aiki ne bisa ga koken da Abubakar Musa ya kai na cewa ana daurawa matarsa aure da wani bayan aurensu bai mutu ba.

A ranar Talata bayan an kama mahaifinnata, Nasiba ta sanar da jaridar Daily Nigerian cewa, Abubakar yayi mata barazanar amfani da dangantakarsa da IGP Adamu don tozartata da danginta.

Amma kuma, a tattaunawar da Abubakar yayi da jaridar Daily Nigerian, ya musanta ikirarin Nasiba kuma ya ce babu wata danagntaka tsakaninsa da IGP din.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: DSS ta bayyana dalilin da yasa ba ta saki Sowore ba

Akan zancen kama sirikin nasa, Abubakar ya kai koke ne ta hannun lauyansa, Rilwanu Umar gaban kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna, Ali Janga, a ranar 12 ga watan Nuwamba akan zargin Nasiba da yake da bata masa suna.

Ya kai koken cewa, matarsa Nasiba 'ya ga Sani Dauda ta je shafinta na Instagram inda ta tozarta shi tare da ci masa mutunci. Kalaman da tayi amfani dasu kuwa a kansa sun kawo tozarci tare da jawo masa illa ga mutuncinsa.

Abubakar ya bayyana yadda Nasiba ta kai kararsa gaban kotu da bukatar su yi Khul'i don rabuwar aurensu. Bayan da kotu ta aminta da hakan, sai Nasiba ta bashi dubu hamsin, hakan kuwa yaci karo da dokar Khul'in domin kuwa a shari'ance kamata yayi ta biyasa duk kudin da ya kashe na aurenta wanda zai bashi damar auro wata mace kamarta.

Rashin gamsuwa da hukuncin kotun yasa Abubakar ya daukaka kara. Bayan nan sai Nasiba ta shigar da karararrki ga kotu har biyu amma kafin a yi shari'ar, sai kwatsam yaji daurin auren Nasiba da Abdullahi Kumali.

A yayin daurin auren ne wani Usman Abdullahi Tela ya je tare da sanarwa da mutane ba halastaccen aure za a daura ba domin kuwa akwai aure a kan amarya, lamarin da yasa 'yan sanda suka yi awon gaba da Usman Tela.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel