Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben Gwamna Emmanuel

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben Gwamna Emmanuel

- Kotun daukaka kara da ke zama a Calabar ta tabbatar da nasarar Udom Emmanuel a matsayin zababben gwamnan jihar Akwa Ibom

- Dan takarar jam'iyyar APC, Mista Nsima Ekere ne ya daukaka kara kan hukuncin kotun sauraron karar zabe da aka yanke a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba a Oyo wacce ta kori karar da ya shigar na kalubalantar zaben

- Kotun daukaka karar ta fara tabbatar da hukuncin kotun zabe na watsi da takardun da mai karar ya cike

Kotun daukaka kara da ke zama a Calabar a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba ta tabbatar da nasarar Udom Emmanuel a matsayin zababben gwamnan jihar Akwa Ibom.

Gwamna Emmanuel na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya kayar da Mista Nsima Ekere na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

An daukaka kara ne a kan hukuncin kotun sauraron karar zabe da aka yanke a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba a Oyo wacce ta kori karar da Ekere ya shigar na kalubalantar zaben.

Da take zartar da hukunci a karar da aka daukaka, kwamitin mutum biyar na kotun ta bayar da hukuncinta akan dukkanin lamuran da jam’iyyun suka gabatar a kararsu.

Kotun daukaka karar ta fara tabbatar da hukuncin kotun zabe na watsi da takardun da mai karar ya cike inda ta nuna cewa dukkanin takardun sun kasance na jama’a ne sannan cewa ba za a iya aiki da su ba.

Bugu da kari, kan ko kotun zaben ta yi daidai wajen cewa mai karar bai gabatar da gamsasshen hujja domin tabbatar da kararsu ba, kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin kotun zaben sannan ta riki binciken kotun zaben kan hujjoji.

KU KARANTA KUMA: Rufe iyakokin Najeriya: Majalisa ta bukaci Kwastam da ta dakatar da batun haramta raba mai ga wasu garuruwa

Kotun ta tabbatar da nasarar Udom Emmanuel a matsayin gwamnan jihar Akwa Ibom sannan ta ci tarar mai karar naira 500,000.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel