Ana Batun Yanke Mazakuta a Kano, Likitoci Sun Dasa wa Wani Mutum Azzakari
- Likitoci a ƙasar Vietnam sun yi nasarar gudanar da aikin dasa mazakuta ga wani mutum mai shekaru 43 ta amfani da sashen jikin wani da ya mutu
- An gudanar da aikin ne bayan an cire wani ɓangare na mazakutar mutumin shekaru huɗu da suka gabata, kuma likitoci sun tabbatar ya dace a aikin
- Asibitin ya ce maras lafiyar na ci gaba da samun sauƙi, yayin da ake bibiyar yadda sabon sashen jikin zai ci gaba da aiki a nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Hanoi, Vietnam – Wasu likitoci a ƙasar Vietnam sun samu nasarar gudanar da aikin dasa azzakari ga wani mutum mai shekaru 43, lamarin da ya zama irinsa na farko a tarihin ƙasar.
An yi amfani da mazakutar wani mutum da ya rasu sakamakon mutuwar ƙwaƙwalwa wajen gudanar da aikin bayan ƙwararrun likitoci sun tantance lafiyar maras mutumin da kuma dacewarsa da irin tiyatar.

Source: Getty Images
Yahoo News ta rahoto cewa mutumin ya taɓa yin tiyatar cire wani ɓangare na mazakutarsa shekaru huɗu da suka gabata a Asibitin Viet Duc Friendship da ke Hanoi.
Yadda aka gudanar da aikin
Darakta na cibiyar kula da lafiyar maza ta asibitin, Farfesa Nguyen Quang, ya ce aikin ya haɗa da sake gina muhimman sassan mazakutar tare da haɗa ƙananan jijiyoyin jini da jijiyoyin motsi ta hanyar amfani da fasahar tiyata ta zamani.
Ya bayyana cewa aikin ya buƙaci matuƙar ƙwarewa domin tabbatar da sabon sashen jikin ya haɗu yadda ya kamata tare da ba maras lafiyar damar samun sauƙi.
Shugaban asibitin, Dr. Duong Duc Hung, ya ce ƙungiyar likitocin ta shafe watanni tana shirye-shiryen aikin tare da nazarin irin ayyukan da aka yi a wasu ƙasashe kafin su aiwatar da shi.

Source: Getty Images
Maras lafiyar na samun sauƙi
Likitocin sun ce maras lafiyar na ci gaba da murmurewa cikin yanayi mai kyau, kuma babu wata matsala da aka gani tun bayan aikin.
Sai dai sun bayyana cewa za a ci gaba da sanya ido domin tabbatar da ko jin motsi, ƙarfin mazakuta da kuma aikin fitsari za su dawo yadda ya kamata, tare da lura da alamun da ka iya nuna jiki ya ƙi karɓar sabon sashen.
The Independent ta wallafa cewa rahotannin likitanci na duniya sun nuna cewa kafin wannan aiki, an samu nasarar irin wannan tiyata sau biyar kacal a faɗin duniya.
An yanke azzakari a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wata mata da ake zargin ta caka wa saurayinta wuƙa tare da yanke masa mazakuta gaba ɗaya.
Lamarin ya faru ne a yankin Badawa, inda rundunar ta ce wanda aka kai wa harin ya samu munanan raunuka kuma yana karɓar magani a asibiti.
'Yan sanda sun ce sun fara gudanar da bincike domin gano musabbabin harin, yayin da ake ci gaba da tsare matar da ake zargi.
Asali: Legit.ng

