An Tsinci Gawar Malami a Yashe, an Ce Wasu ne Suka Daɓa Masa Wuka har Lahira

An Tsinci Gawar Malami a Yashe, an Ce Wasu ne Suka Daɓa Masa Wuka har Lahira

  • An gano gawar wani limamin cocin Katolika a Ajaokuta, bayan an daba masa wuka tare da yi masa munanan raunuka
  • Rundunar 'yan sandan Kogi ta ce jami'anta sun garzaya wurin da aka tsinci gawar, suka kai ta asibiti, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa
  • 'Yan sanda sun ce suna gudanar da bincike domin gano tare da cafke wadanda suka kashe limamin, kafin mika shari'ar zuwa sashen binciken manyan laifuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ajaokuta, Kogi - An gano gawar wani limamin cocin Katolika, Fasto Samuel Opeyemi, a yankin Ajaokuta da ke Kogi bayan wasu mutane sun kashe shi.

Kafin rasuwarsa, marigayin yana gudanar da aikin limanci a cocin St. Mary's Catholic Church da ke garin Egbe, inda yake yi wa mabiya hidima.

An tsinci gawar fasto a Kogi
Taswirar jihar Kogi da aka kashe fasto. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahotanni sun ce an daba wa Fasto Opeyemi wuka sau da dama, sannan aka tsinci gawarsa a gefen hanya a yankin Ajaokuta da ke Kogi, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

An kama dan shekara 20 da zargin ba 'yan bindiga makamai

Martanin yan sanda kan lamarin

Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar 'yan sandan Kogi, ASP Afusat Salihu, ta tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa da ta fitar.

Ta bayyana cewa rundunar ta samu rahoton gano gawar wani namiji da ba a san ko wane ne ba a bakin titin Church Road da ke Ajaokuta.

Sanarwar ta ce:

"Jami'an tsaro sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka tarar cewa mamacin ya samu munanan sara da adda a kansa.
"Daga nan aka kai gawarsa Asibitin ASCL, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa, sannan aka kai gawar dakin ajiye gawa domin gudanar da binciken gano musabbabin mutuwa, daga baya an gano mamacin a matsayin Fasto Samuel Opeyemi na Cocin St. Paul Parish da ke Ayetoro Gbede, ƙaramar hukumar Ijumu, Kogi.
"A halin yanzu ana ci gaba da bincike kan lamarin, tare da ƙoƙarin cafke waɗanda ake zargi da hannu a kisan."

Kara karanta wannan

'Babu yan bindiga a Niger': Gwamnati ta gano yadda aka samu rashin tsaro

An kashe wani fasto a Kogi
Sufeta-janar na sanda a Najeriya, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Yadda aka samu gawar fasto a Kogi

Rundunar ta ce da isar jami'ai wurin, sun tarar mamacin na dauke da munanan raunukan sara da adda a kansa, sannan aka kai gawarsa asibitin ASCL.

Likitan da ya duba gawar ya tabbatar da rasuwarsa, daga bisani aka ajiye gawar a dakin ajiye gawa domin gudanar da binciken gawar, cewar Sahara Reporters.

Bayan tantancewa, an tabbatar cewa mamacin Fasto Samuel Opeyemi ne daga cocin St. Paul Parish da ke Ayetoro Gbede a karamar hukumar Ijumu, yayin da 'yan sanda ke ci gaba da bincike domin cafke wadanda suka aikata kisan.

An samu gawar babban jami'in FRSC

Mun ba ku labarin cewa ana zargin ‘yan bindiga sun tare motar da ke ɗauke da gawar tsohon babban jami’in FRSC, Augustine O. Ikwue, a jihar Kogi.

Rahotanni sun nuna cewa gawar da mutane tara, ciki har da jami’an FRSC biyu, sun fada hannun masu garkuwa da mutane.

Sai dai bayanai sun nuna cewa daga baya an gano gawar marigayin a garin Ejule, inda aka mika ta ga iyalansa domin yi masa jana'iza yadda ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.