An Yi wa Dan APC Mai Tallata Tinubu Jina Jina, za a Farauci Wadanda Suka Daka Shi

An Yi wa Dan APC Mai Tallata Tinubu Jina Jina, za a Farauci Wadanda Suka Daka Shi

  • Gwamnatin jihar Delta ta umarci jami'an tsaro su gano tare da kama mutanen da suka kai hari kan Simon Mudi, hadimin gwamna Sheriff Oborevwori
  • An kai harin ne yayin taron masu ruwa da tsaki na APC a Delta ta Tsakiya, inda aka ji wa Simon Mudi da wasu raunuka masu tsanani
  • Tsohon minista Solomon Dalung ya ce Simon Mudi na ci gaba da samun sauki, yana kuma godiya ga 'yan Najeriya da suka yi masa addu'a da nuna goyon baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta – Gwamnatin jihar Delta ta umarci hukumomin tsaro su gaggauta ganowa tare da kama duk mutanen da suka kai hari kan hadimin gwamnan Delta, Simon Mudi, wanda aka fi sani da Temple.

An kai harin ne a ranar Lahadi yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a yankin Delta ta Tsakiya da aka gudanar a Effurun a karamar hukumar Uvwie.

Kara karanta wannan

An daure dalibin Jami'ar Jos, an masa duka da katako sai da ya mutu kan waya

Tempele da aka yi wa duka kan APC
Hadimin gwamnan Delta da aka yi wa duka a taron APC. Hoto: Solomon Dalung
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa gwamnatin jihar ta bayyana harin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, tana mai cewa ya zama barazana ga zaman lafiya da tsaron jama'a.

Umarnin da gwamna ya bayar

Kwamishinan ayyuka da yaɗa labarai na jihar, Charles Aniagwu, ya ce gwamnatin ta damu matuka da bidiyoyin da suka bazu a kafafen sada zumunta kan yadda aka yi wa Simon Mudi mummunan duka.

Ya bayyana cewa gwamnatin gwamna Sheriff Oborevwori ba za ta lamunci tashin hankali ko daukar doka a hannu ba, tare da gargadin cewa duk masu hannu a harin za su fuskanci hukunci.

Aniagwu ya ce:

"Gwamna Sheriff Oborevwori ya umarci jami'an tsaro su gano, su kama tare da gurfanar da duk wadanda suka shiga wannan hari.
"Abin da aka yi wa Simon Mudi abin Allah wadai ne."

Rahotanni sun ce Simon Mudi ya samu munanan raunuka bayan wasu matasa dauke da makamai sun kai masa hari, yayin da aka kuma ce kwamishinan ayyuka na birane da manyan hanyoyi, Reuben Izeze, shi ma ya fuskanci hari.

Kara karanta wannan

'Babu yan bindiga a Niger': Gwamnati ta gano yadda aka samu rashin tsaro

Bayanin Solomon Dalung

Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana cewa ya samu labarin Simon Mudi na karbar magani a asibiti kuma yana samun sauki.

Dalung ya gode wa 'yan Najeriya bisa addu'o'i, sakonnin fatan alheri da goyon bayan da suka nuna bayan harin.

A sakon da ya wallafa a Facebook, ya ce:

"Raunukan da ya samu za su dauki lokaci kafin su warke, amma addu'o'i da kulawar da 'yan Najeriya suka nuna sun ba shi karfin gwiwa. Yana godiya ga duk wadanda suka tsaya masa ba tare da la'akari da bambancin siyasa ba."
Barista Solomon Dalung
Solomon Dalung yayin hira da 'yan jarida. Hoto: Solomon Dalung
Source: Getty Images

A sanarwar da ya fitar da farko, Solomon Dalung ya ce wasu labaru da ba a tantance ba sun nuna cewa an yi wa hadimin gwamnan duka ne saboda ya tallata Bola Tinubu.

An kashe dalibi a Jos

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu biyu daga cikin mutum hudu da 'yan sandan jihar Plateau suka kama kan kisan dalibin Jami'ar Jos, Ibrahim Mabaye, sun bayyana yadda suka azabtar da shi har ya mutu.

Kara karanta wannan

An kama matashi da buhunan abinci da wasu muhimman kaya zai kai wa Boko Haram

An yi wa dalibin mai shekaru 25 duka har ya mutu ne a yankin Ring da ke Jos ta Arewa bisa zargin satar wayar iPhone 12 a dakin wani matashi.

Rundunar 'yan sanda ta ce wasu dalibai sun kai shi Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jos domin ceto rayuwarsa, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarsa bayan isa asibitin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng