Addu'ar mutuwar Buhari: Kakakin Osinbajo ya tambayi marubuci manyan tambayoyi 4

Addu'ar mutuwar Buhari: Kakakin Osinbajo ya tambayi marubuci manyan tambayoyi 4

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, ya musanta zargin da ake na cewa, ubangidansa ya ziyarci majami'ar RCCG inda shi da jam'in suka yi addua'ar mutuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Akande, wanda mai bayar da shawara na musamman ne ga shugaban kasa a kan yada labarai, ya ce wannan takardar an yi ta ne don mayar da martani ga Dr. Festus Adedayo.

A wani rubutu da aka wallafa a ranar Lahadi a wasu jaridu, Adedayo ya ce mataimakin shugaban kasa wanda babban fasto ne ya jagoranci mutanen da suka halarci majami'ar a kan addu'ar mutuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin da ya yi tafiya don jinya.

DUBA WANNAN: 'APC' ta dakatar da Gwamna Obaseki da mataimakinsa a kan zargin za su koma PDP

Hakan kuwa ya koma kunnen shugaban kasar, lamarin da ya jawo baraka a dangantakarsu.

A mayar da martanin da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar ya yi, ya kalubalanci Adedayo da ya fadi majami'ar da aka yi wannan addu'ar.

"A ina a jihar Ogun aka yi addu'ar kuma yaushe?

A majami'a ne ko akwai faifan sautin muryar?

Wadanne sanannun fastocin ne aka yi addu'ar tare da su, bayyana sunayensu?.

Wanene babban na hannun damar Buharin da ya yi bayyanar bazata yayin da ake addu'ar kuma ya kai labarin ga shugaba Buhari?"

Akande ya kara da kalubalantar ikirarin Adedayo da yace mataimakin shugaban kasar na da wata manufar da ya tura sunan Jastis Walter Onnoghen ga majalisar dattawa don tabbatar dashi a matsayin shugaban alkalan Najeriya.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar ya ce, abin haushi ne a ce wasu sun dau nauyin mutane don assasa wutar rigima tsakanin shugaban kasar da mataimakinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel