"Shiri ne": Yadda Aka Kashe Babban Soja Mahaddacin Kur'ani Mai Shirin Kafa Tarihi
- Wasu mazauna Kurudu da makwabta sun bayyana yadda aka kashe Kanal Abdulrasaq Abdussalam Ude a Abuja
- Rahotanni sun ce maharan sun yi ƙoƙarin yin garkuwa da jami’in, amma ya yi musu turjiya wanda hakan ya sanya suka bindige shi
- Wani danginsa ya ce ba yunkurin sace shi aka yi ba, yana zargin an yi wa Kanal Ude kisan gilla da gangan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mazauna yankin Kurudu da makwabta sun bayyana yadda aka kashe babban jami’in leƙen asirin soja, Kanal Abdulrasaq Abdussalam Ude.
'Yan bindiga sun kashe marigayin ne yayin da yake komawa gidansa da ke yankin Kurudu a ƙaramar hukumar Abuja ta babban birnin tarayya.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce an kai wa Kanal Ude hari ne jim kaɗan bayan ya isa gidansa a yammacin ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2026.
Direbansa da mai gadinsa ma sun samu raunukan harbin bindiga yayin harin da 'yan bindigan suka kai.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi ƙoƙarin yin garkuwa da Kanal Ude, amma ya yi musu turjiya.
“Ya yi musu turjiya. Bisa bayanan da masu bincike suka tattara, suna son su tafi da shi ne, amma ya ƙi amincewa. Abin takaici, ya rasa ransa sakamakon haka,” wata majiya da ke da masaniya kan binciken farko ta ce:
Yadda aka kashe Kanal Ude
Bayan sun kasa tafiya da shi, ana zargin maharan sun harbe Kanal Ude sau da dama kafin su tsere daga wurin.
An garzaya da matarsa, direbansa da mai gadinsa zuwa asibiti bayan harin, inda suke karɓar magani sakamakon raunukan harbin bindiga daban-daban da suka samu.
Sai dai a wani rubutu da ya wallafa a Facebook ranar Laraba, wani Ali Chukwudi, wanda ya bayyana kansa a matsayin surukin marigayin, ya ce kisan ya kasance shiri ne da aka tsara, ba yunkurin yin garkuwa da shi da bai yi nasara ba.
“Jiya Najeriya ta rasa ɗaya daga cikin fitattun ‘ya’yanta. Surukina, Kanal Abdulrazaq Abdulkareem Ude, babban jami’in leƙen asiri wanda ya shafe shekaru yana kare wannan ƙasa, ba a kashe shi ba ne yayin da yake ƙoƙarin hana a yi garkuwa da shi, kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana. Da gangan aka tsara kuma aka hallaka shi."
Dan uwan matarsa ya yi zargi
Chukwudi ya ce maharan sun harbe Kanal Ude a kai, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa. Ya ƙara da cewa an harbi matar Kanal Ude, wadda ya bayyana a matsayin ‘yar uwarsa, a ƙafa.
A cewarsa, direban marigayin da mai gadin ƙofar gidansa ma sun samu raunukan harbi a ƙafafunsu.
“Yayin da nake rubuta wannan, ‘yar uwata tana asibiti tana fafutukar neman tsira da ranta. in ji Chukwudi.
Ya ce marigayi Kanal Ude ya yi wa Najeriya hidima cikin aminci tsawon shekaru, kuma saura ‘yan watanni a kara masa girma wani matsayi da ya ce ya cancanta.
Chukwudi ya bayyana kisan a matsayin hari kai tsaye kan wani jami’in soja mai kishin ƙasa.
Tarihin ayyukan Kanal Ude
Marigayi Kanal Ude, wanda ɗan asalin jihar Enugu ne, ya riƙe muƙamai masu muhimmanci da dama a fannin leƙen asiri da yaƙi da ta’addanci a rundunar sojin Najeriya.
Ya shiga ayyukan yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. An kuma tura shi wasu ayyuka na musamman a ƙasashen Chadi da Faransa, inda ya bayar da gudummawa wajen haɗin gwiwar leƙen asiri da tsaro.

Source: Twitter
Marigayin na shirin samun karin girma zuwa matsayin Birgediya Janar, wanda hakan zai sanya ya musulmi na farko dan kabilar Igbo da ya taba samun matsayin.
An binne gawar Kanal Ude ranar Talata bayan an gudanar da sallar jana’izarsa a Masallacin Mambilla da ke Abuja bisa koyarwar addinin Musulunci.
'Yan Boko Haram na shirin kai hare-hare
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta yi gargadin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram na shirin kai manyan hare-hare a jihohin Adamawa da Borno.
Hukumar DSS ta yi gargadin cewa ana shirin kai hare-haren ne a ƙaramar hukumar Michika ta jihar Adamawa da kuma ƙaramar hukumar Askira-Uba ta jihar Borno.
Asali: Legit.ng


