Na fi kaunar mijina idan yana talauci - Wata mata ta bayyana sirrinta

Na fi kaunar mijina idan yana talauci - Wata mata ta bayyana sirrinta

- Joro Olumofin, kwararre ne a fannin zamantakewar aure da masoya, ya bayyana sakon da wata matar aure ta aika masa dashi

- Matar ta bayyana yadda take addu'ar mijinta ya talauce don sun fi zaman lafiya

- Yafi kula da ita tare da nuna mata soyayya tamkar a fina-finai matukar bashi da kudi

Kwararre a fannin zamantakewa, Joro Olumofin ya bayyana wani sako da wata mata ta aika masa ta yanar gizo. A sakon matar ta bayyana cewa ta fi son mijinta idan bashi da kudi.

Ga abinda matar ta rubuta: "Barka dai Joro, ban san mene ne yake damuna ba, na farawa mijina mummunar addu'a yau a coci, kada mutane su ce ni mayya ce, gaskiya lokacin da mijina bashi da kudi na fi son shi, kuma shima yafi mutunta ni."

"Idan bashi da kudi, yana zuwa coci sosai, Joro mijina rabon da ya je coci tun watan Fabrairu saboda ya samu kudi, mutane da yawa a cocinmu suna yada jita-jitar mun rabu dashi abun yana bani haushi sosai."

KU KARANTA: Musulunci ya samu karuwa: Gari guda sukutum sun Musulunta baki dayan su

"A makon da ya gabata sai dana zubda hawaye, mijina ne ke tambayar da na dalilin da yasa yake sa dogon wando zuwa makaranta, hakan na nufi bai san dan mu ya shiga aji hudu na sakandire ba, a takaice dai bani da miji, a takardu ne kawai nake da aure, akan me ba zan yi masa fatan kudin ya kare ba?"

"Na ga kwaroron roba a motarsa, cikin rigarsa, ina fatan ubangiji ya kwace arzikin na shi. Ina da aikina da kudina amma na rasa abokin rayuwa, ni kadai ce. A yanzu haka baya gida, karamar yarinyarmu tsoronsa take ji saboda bata san mahaifinta ba ne, bai kuma damu da hakan ba. Idan ba shi da kudi yana da kirki kuma ya iya soyayya kamar a fina-finai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel