Tinubu Ya Fadi Yadda Za a Hana Gwamnoni Amfani da 'Yan Sanda Jihohi ba Bisa Ka'ida ba
- Shugaba Bola Tinubu ya ce tsarin ’yan sandan jiha da ake shirin kafawa zai kunshi matakan da za su hana gwamnonin jihohi amfani da rundunar ba bisa ka’ida ba
- Ya ce gwamnatin tarayya na kokarin kara karfin hukumomin tsaro, tare da fadada rundunar sojojin Najeriya domin su iya mayar da martani cikin gaggawa
- Tinubu ya kuma ce gwamnati ba za ta tattauna da masu garkuwa da mutane ba, bayan ceto dalibai da malamai da aka sace a karamar hukumar Oriire
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa tsarin ’yan sandan jiha da ake shirin kafawa zai kunshi matakan kariya da za su hana gwamnonin jihohi yin amfani da rundunar ba bisa ka’ida ba.
Tinubu ya kuma ce gwamnatin tarayya ta dukufa wajen kara karfi da inganta tsarin tsaron Najeriya domin tunkarar matsalolin rashin tsaro a fadin kasar.

Source: Twitter
The Cable ta ce shugaban kasar ya bayyana haka ne ranar Alhamis yayin da ya karbi sarakunan gargajiya karkashin Majalisar Sarakunan Jihar Oyo, karkashin jagorancin Olubadan na Ibadanland, Rashidi Ladoja, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Matakan kare tsarin ’yan sanda
Tinubu ya ce tsarin ’yan sandan jiha zai kasance karkashin dokoki da matakan sa ido, yayin da sarakunan gargajiya za su taka rawa wajen tabbatar da daukar alhaki.
“Za a kafa ’yan sandan jiha. Za a samar da matakan da za su hana yin amfani da rundunar ba bisa ka’ida ba. Za mu kare tsarin daga cin zarafi, kuma ku sarakunan gargajiya ma za ku taka rawa.”
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaban kasar ya ce gwamnati na kuma kara karfi da inganta ayyukan masu gadin dazuka domin su rika bin diddigin masu laifi a cikin dazuka.
“Muna kuma kara karfi da inganta kwarewar masu gadin dazuka. Ba wai aikinsu kawai shi ne korar barewa da sauran dabbobi ba. Za mu sa su rika bin masu laifi tare da tunkararsu a dazuka daban-daban.”
An kara rundunonin sojoji
Tinubu ya ce gwamnatin tarayya ta kirkiri karin rundunonin sojojin Najeriya guda hudu, wanda ya kai adadin rundunonin zuwa 12, The Punch ta kawo labarin.
Ya bayyana cewa matakin zai bai wa sojoji damar mayar da martani cikin sauri ga barazanar tsaro a sassan Najeriya.
A cewarsa, fadada tsarin rundunar sojin zai kara wa jami’an kwarin gwiwa tare da inganta kokarinsu na shawo kan kalubalen tsaron kasar.
Tinubu ya yabawa sojoji
Shugaban kasar ya yabawa jami’an tsaro kan ceto dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo.
Tinubu ya ce aikin ceton ya yi nasara ne saboda gwamnatin tarayya ta ki amincewa da tattaunawa da masu garkuwa da mutanen.

Source: Twitter
“Ina taya ku murna kan nasarar aikin ceto da aka yi a Oriire. Ina ganin mun samu nasarar ne da goyon bayanku da addu’o’inku. Na yarda da ku cewa ya kamata mu yabawa maza da mata na rundunar sojojin kasar saboda kyakkyawan aikin da suka yi.”
“A madadinsu, na karbi sakonku kuma zan isar musu da shi.”
- Shugaba Bola Tinubu
Shawarar Tinubu ga gwamnoni
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi su mayar da hankali wajen gina hanyoyi da sauran muhimman ababen more rayuwa.
Mai girma Bola Tinubu ya bukaci gina hanyoyi ne maimakon gina gadar sama da ayyukan da ba su da amfani sosai ga jama'a.
Asali: Legit.ng


