Fallasa: Asirin wasu ma'aikatan NNPC ya tonu

Fallasa: Asirin wasu ma'aikatan NNPC ya tonu

Rahoton kwamitin wucin-gadi na majalisar dattawa akan fashewar bututun mai a kasar nan ya nuna cewa, wasu jami'an NNPC ne ke hada kai da masu satar man fetur din don aiwatar da laifin.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a jawabinsa bayan karbar rahoton, yace duk jami'in da aka kama yana hada kai da 'yan ta'adda wajen fasa bututun man fetur za a hukunta shi

Kamar yadda Lawan yace, ya zama dole kwamitin majalisar ya gayyaci matatar man fetur din ta kasa don kara duba matakan tabbatar da tsaron bututun man fetur da ke fadin kasar nan.

Shugaban majalisar ya kara da cewa, majalisar zata gyara dokar cibiyar tantance nason man fetur ta kasa don hana waddakar da masu fasa bututu suke yi wacce ke kawo gobara da mace-macen rayuka.

DUBA WANNAN: Babbar mota ta murkushe mutum 20 sakamakon bin ta da 'yan sanda suke

Ya ce: "Kwamitin majalisar zai gayyaci NNPC din don sanin wanne mataki suka dauka a cikin shekarun baya akan kare bututun man fetur. Wadanne matakai ne a halin yanzu suke amfani dasu kuma akwai bukatar dubasu tare da yarda dasu?"

"Wannan masa'anta ce ta biliyoyin dalolin kudi. Da ganganci mutane ke abu amma sai su ce hatsari ne. Wadanda wutar ta kama dasu tare da wadanda suka je samun nasu ne ke rasa rayukansu, hakan ba zai yuwu ba,"

"Dole ne ya zamo da hukunci a kan wadannan laifukan. Bayan mun samu matsaya akan dokokin, dole ne kwamitin ya bibiyesu, Idan aka gyara dokar NOSRDRA, za a samu sauki. Mu yi wannan abu ne don hana cigaba da aukuwarsa, mu datse 'yan ta'addan."

A gudummawar Sanata Chukwuka Utazi akan lamarin, ya dora laifin fasa bututun man fetur din a kan wasu jami'an NNPC din. 'Yan majalisar sun yi kira da a hukunta duk jami'in da aka kama da laifin hada kai da 'yan ta'addan wajen fasa bututun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel