Sardaunan Sokoto, Abubakar Alhaji Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Sardaunan Sokoto, Abubakar Alhaji Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An samu rahoton da ya tabbatar da rasuwar tsohon babban kwamishinan Najeriya a Birtaniya, Alhaji Abubakar Alhaji a babban birnin tarayya
  • Wata majiya ta bayar da tabbacin cewa tsohon dan siyasar da ya dade ya na yi wa Najeriya hidima ya rasu da safiyar ranar Alhamis
  • Rahotanni sun ce ya rasu ne a wani asibiti da ke Abuja bayan ya dade yana karbar, inda ake jiran wasu muhimman bayanai daga bakin iyalansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Dattijon ɗan siyasa kuma tsohon jami'in diflomasiyyar, Abubakar Alhaji ya rasu ne da safiyar ranar Alhamis 29 ga watan Yuli, 2026 a wani asibiti da ke Abuja.

Wata majiya mai tusge ce ta sanar da rasuwar, kuma ta tabbatar da cewa marigayin yana karɓar kulawar likitoci kafin rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Likitan El Rufa'i ya rubuta zungureriyar takarda, ya yi bayani kan zargin ICPC

Basaraken Sokoto ya rasu
tsohon babban kwamishinan Najeriya a Birtaniya, Alhaji Abubakar Alhaji Hoto: Almustapha Jadadi
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ya wallafa cewa marigayi Abubakar Alhaji ya taba zama Babban Kwamishinan Najeriya a Birtaniya, inda ya wakilci ƙasar a matsayin babban jami'in diflomasiyya.

Yadda Sardauna ya taimaki Najeriya

Jaridar Aminiya ta kawo labaran cewa Abubakar Alhaji ya shahara da gudummawar da ya bayar a harkokin hidimar gwamnati da ci gaban ƙasa a tsawon shekarun da ya yi yana aiki.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a fitar da cikakken bayani kan musabbabin rasuwarsa ba, sai dai an san ya rasu ne a Abuja kuma a asibiti.

Ana sa ran iyalansa tare da hukumomin da abin ya shafa za su sanar da ƙarin bayani game da shirye-shiryen jana'izarsa da sauran bayanai nan gaba.

Waye Sardaunan Sokoto

An haifi Alhaji Abubakar Alhaji a gidan Malam Muhammad Sani, wanda aka fi sani da Alhaji Alhaji saboda an haife shi a ranar Sallah.

Ya fara karatun sakandare a jihar Kano kafin ya koma kwalejin Gwamnati ta Katsina domin ci gaba da zurfafa iliminsa.

Kara karanta wannan

Jigon ADC: 'Hari kan mahaifar mataimakin gwamna ya nuna ba mafaka a Sokoto'

Daga bisani ya yi karatu a Bournemouth College of Commerce da kuma Jami'ar Reading da ke jihar Berkshire a Birtaniya, inda ya samu digiri a fannin Tattalin Arziki da Siyasa.

Ana jiran bayanai game da jana'izar Sardaunan Sokoto
Taswirar jihar Sokoto da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Haka kuma ya halarci ƙarin kwasa-kwasai a Hague Institute of Social Services da kuma IMF Institute da ke birnin Washington.

Abubakar Alhaji fitaccen jami'in gudanarwa ne a Najeriya wanda ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Tsare-tsare da Kuɗi. Haka kuma yana riƙe da sarautar Sardaunan Sakkwato.

Marigayin ya shafe shekaru masu yawa yana aiki a matsayin Babban Sakataren Gwamnatiinda ya yi aiki ƙarƙashin gwamnatoci daban-daban na Najeriya.

Tsohon alkali ya rasu

A baya, mun kawo labarin cewa an shiga jimami da alhini bayan an fitar da sanarwar rasuwar tsohon alkalin Babbar Kotun Tarayya daga jihar Borno da ke Arewacin Najeriya.

Mai shari'a Babagana Ashigar, ya rasu a Maiduguri bayan gajeruwar rashin lafiya, lamarin da ya jawo alhini tsakanin ma'aikatan shari'a da iyalansa da sauran yan uwa da abokan arziki.

An yi jana'izarsa bisa koyarwar addinin Musulunci, yayin da Babbar Kotun Tarayya ta bayyana cewa ya yi aiki da gaskiya a lokacin da ake ci gaba da yi masa addu'ar rahamar Allah SWT.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng