Innalillahi: Saurayi ya mayar da budurwar shi abar bauta ya fara bauta mata

Innalillahi: Saurayi ya mayar da budurwar shi abar bauta ya fara bauta mata

- Wata hira tsakanin saurayi da budurwa ta ba wa mutane da yawa mamaki

- A hirar saurayin na neman soyayyar budurwar ne amma ta wani salo da ba a taba ji ba

- Ya bukaci budurwar da ta zama 'ubangijinsa' don zai bauta mata tare da neman bukatunsa daga wajenta

Wata hira tsakanin wani saurayi da budurwa na ta yawo a kafar sada zumunta ta Twitter saboda yadda hirar ta kasance banbarakwai babu kan gado, ko kuma mu ce mutane ba su saba ganin irin wannan hirar ba.

A hirar, saurayin yana neman soyayyar budurwar ne ta hanyar da ba a saba gani ba. Ya bukaci da ta bashi dama ya bauta mata kuma yana da burin ta zama 'Ubangijinsa'. Ya kara da bayyana mata cewa, ya yi imanin cewa yakamata ta zama 'Ubangijin sa kuma addininsa'.

A maida martanin budurwar ta nuna tana tsammanin wasa yake da farko amma daga baya ya bayyana mata shi komai da ya fada da gaske yake.

KU KARANTA: Ina jin mutuwa zanyi - 'Yar aiki a kasar Saudiyya ta bayyana yadda ubangidanta yake cin zarafinta a wani bidiyo

Ma'abota amfani da kafar sada zumuntar ta Twitter sun cika da mamakin wannan tsantsar soyayyar da saurayin ke nunawa budurwar inda suka dinga tsokaci akai.

Ga sakon da saurayin ya tura wa budurwar: "Zai miki banbarakwai, amma zan so bauta miki, ina fatan zamu iya magana. Ban so tsorata ki ba amma na dade ina neman kyakyawar mace da zata amince ta zama 'Ubangijina'. Ina kallon wani addini ne da zan bauta miki kuma in miki addu'a. Na yarda cewa addini mace ce, kuma a tunani na shine kadai addinin da zan iya yi."

"Gaskiya na yarda ke ce 'ubangiji' saboda kyan ki. Kina da kyau kuma ina ji karfin ikonki." Cewar saurayin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel