Babbar mota ta murkushe mutum 20 sakamakon bin ta da 'yan sanda suke

Babbar mota ta murkushe mutum 20 sakamakon bin ta da 'yan sanda suke

A kalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu bayan ‘yan sanda suka biyo da babbar mota dankare da amfanin gona. Babbar motar ta murkushe Keke Napep masu yawa a ranar ranar Talata.

Kamar yadda rahoton ya nuna, lamarin ya faru ne gadar Vunokilang wacce aka sani da Hayin Gada a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Wani mazaunin Vunokilang, malam Umar Shehu, wanda ya turawa wakilin Laila News hotunan wajen da abin ya faru, yace ya shiga cikin ayarin mutanen da suka kwaashe gawawwakin zuwa asibiti kwararru da ke Yola.

DUBA WANNAN: Kotu ta yi barazanar fatali da shari'ar tsohuwar ministar man fetur

Kamar yadda ya bayyana, jami’an ‘yan sanda sun bada bayanin cewa, suna biye da babbar motar ne dauke da kayyaykin da suke zargin sun hada da shinkafar gwamnati, abinda ya kawo aukuwar mummunan lamarin da yayi sanadin rayuka da yawa.

“Amma kuma babu shinkafar ‘yar gwamnati a cikin babbar motar, amfanin gona ne dankare. Direban yace, suna biye dashi ne saboda ya ki basu na shan ruwa akan hanyar da suka tsaresa don duba kayan cikin motar,” Umar yace.

Wani mazaunin yankin mai suna Fidelis Jockthan yacwe, ya kirga Keke Napep masu tarin yawa da babbar motar ta murkushe. Ya tabbatar da cewa, hatsarin ya kawo cushewar babbar gadar Yola ta yadda babu shige da ficen ababen hawa har zuwa wajen jami’ar kimiyya ta Modibbo Adama.

Daya daga cikin daliban jami’ar Modibbo Adama mai suna Salisu Ibrahim ya bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya ta yadda hatsarin bai ritsa dashi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel