Babbar Magana: Gwamnatin Tinubu za Ta Zare Tallafin Lantarki a 2027

Babbar Magana: Gwamnatin Tinubu za Ta Zare Tallafin Lantarki a 2027

  • Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu tana shirin cire tallafin bangaren wutar lantarki a hankali inda za a fara daga shekarar 2027
  • Game da karin kudin wuta, ministan ya ce ba za a sami karin kudin wuta ba nan take ga masu amfani da wutar lantarki a yau da kullum
  • Ya ce za a cire tallafin ne daki-daki domin tabbatar da cewa ba a hana al'umma amfanin da suke samu ba, tare da daidaita bashin da ake bi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da tsarin janye biyan tallafi a bangaren wutar lantarki da za a fara daga shekarar 2027.

Ministan makamashi, Joseph Tegbe, ne ya bayyana wannan tsari a lokacin wani taro da manema labarai a ranar Juma'a, yayin da yake magana kan bashi da ake babi a bangaren wutar lantarkin.

Kara karanta wannan

An yi wa dan APC mai tallata Tinubu jina jina, za a farauci wadanda suka daka shi

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu da wayoyin wutar lantarki a gefen shi. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa ya ce za a cire tallafin ne a hankali, amma ya tabbatar da cewa 'yan Najeriya ba za su shiga babbar matsala ba.

Haka zalika, Vanguard ta rahoto cewa ministan ya sake jaddada cewa babu wani shiri na kara kudin wutar lantarki nan take bayan zare tallafin.

Bashi ya addabi Najeriya

Sanarwar na zuwa ne yayin da bashin kuɗin da ke kan bangaren wutar lantarki a Najeriya ke ci gaba da ƙaruwa a Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zuwa watan Fabrairun 2024, kuɗin tallafin wutar lantarki ya kai kusan Naira tiriliyan 3, yayin da Ƙungiyar Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki (APGC) ta ce ana bin kamfanonin samar da wutar lantarki bashin kusan Naira tiriliyan 6.5.

Domin fara magance wannan gibin, Shugaba Bola Tinubu ya amince da shirin fitar da takardun bashi na Naira tiriliyan 4 a farkon wannan watan domin biyan tsofaffin basussukan da ke cikin bangaren.

Kara karanta wannan

An daure dalibin Jami'ar Jos, an masa duka da katako sai da ya mutu kan waya

A watan Janairu, gwamnati ta riga ta fitar da kason farko na takardun bashin da ya kai Naira biliyan 501 a karkashin Shirin Rage Basussukan Bangaren Wutar Lantarki na Shugaban Ƙasa.

Ma'aikatan kamfanin TCN
Yadda jami'an kamfanin TCN ke aiki. Hoto: TCN
Source: Facebook

Daga baya, a ranar 20 ga Yulib 2026, an sanar da kashi na biyu na kusan Naira biliyan 729 domin biyan ƙarin basussukan da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarki.

Ana sa ran wannan shirin biyan basussukan zai ba bangaren damar samun kuɗaɗen gudanar da ayyuka cikin sauƙi, ta yadda kamfanonin samar da wutar lantarki za su iya biyan kuɗin aiki, inganta kayayyakin more rayuwa da kuma ƙara ingancin samar da wutar lantarki ga jama'a.

Har ila yau, dakatar da tsarin tallafin wutar lantarki ya yi daidai da shawarwarin Asusun Lamuni na Duniya (IMF), wanda ya sha ba Najeriya shawarar rage tallafin wutar lantarki domin ƙarfafa tattalin arzikin bangaren da kuma rage nauyin kashe kuɗin gwamnati.

Za a horas da matasa 5,000

A wani labarin, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da wani sabon shiri na ƙasada zai horas da matasa 'yan Najeriya 5,000 domin sanya mitar lantarki.

Kara karanta wannan

Tashoshin samar da lantarki sun tsaya cak da aiki, an dauke wuta a fadin kasar Ghana

Ana aiwatar da shirin ne ta hannun Shirin Shugaban Ƙasa na Samar da Na'urorin Auna Wutar Lantarki (PMI), tare da haɗin gwiwar Ma'aikatar Matasa ta Tarayya.

An ce an tsara shirin ne domin cike gibin ƙwararrun ma'aikatan da ake buƙata wajen sanya na'urorin auna wutar lantarki, tare da buɗe ƙarin damammakin da matasa za su taka rawa kai tsaye wajen gina ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng