Kuma dai! An kashe yan sanda 3 a jihar Kaduna

Kuma dai! An kashe yan sanda 3 a jihar Kaduna

Jami'an yan sanda uku dake aiki a Fadan Karshi, karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna sun rasa rayukansu a ranar Talata, 13 ga Nuwamba, 2019.

Wasu yan bindiga sun bindige yan sandan uku ne a kan titi tsakanin Fadan Karshi da Sabon Gida.

Mataimakin shugaban karamar hukumar Sanga, Abubakar Abba, ya tabbatar da aukuwan lamarin ga kamfanin dillancin Labarai NAN a ranar Laraba.

Ya bayyana cewa an ajiye gawarsu a dakin ajiye gawawwaki na Asibiti Gwantu.

"Yan sanda biyu sun mutu a take yayinda daya ya karasa a hanyar zuwa asibiti."

Mataimakin kakakin hukumar yan sandan Kaduna, ASP Suleiman Abubakar, ya tabbatar da labarin kuma ya ce hukumar za tayi tsokaci kan lamarin.

A wani labarin mai kama da haka, An harbe jami'an yan sanda biyu har lahira a garin Otuogidi, karamar hukumar Ogbia ta jihar Bayelsa a ranar Talata, 12 ga Nuwamba, 2019.

Bayan hallakasu, Yan bindigan sun yi awon gaba da makaman yan sandan ana saura kwanaki shida zaben gwamnan jihar da zai gudana ranar Asabar.

An kaiwa yan sandan hari ne a kusa da kwalejin koyan ilmin kiwon lafiya a Ogbia.

Yayinda daya daga cikin yan sandan ya mutu nan take, dayan ya cikasa ne bayan an kaishi asibiti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel